Shugaba Buhari bai taba tauyewa 'yan Najeriya 'yancin addini ba, inji MURIC

Shugaba Buhari bai taba tauyewa 'yan Najeriya 'yancin addini ba, inji MURIC

  • Kungiyar MURIC ta bayyana cewa, Najeriya ba ta take 'yancin addini a gwamnatance a matakan jiha ko tarayya
  • Daraktan MURIC ya bayyana cewa, Shugaba Buhari bai taba take 'yancin addini ba a gwamnatinsa gaba daya
  • Ya kuma yi watsi da masu cewa gwamnatin Amurka ta yi kuskuren cire Najeriya a jerin masu take 'yancin addini

Najeriya - Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Musulunci (MURIC), ta ce gwamnatin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ba ta taba take 'yancin addinai a Najeriya ba.

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, a wata tattaunawa da ya yi da Punch ya ce Amurka ta saka Najeriya cikin jerin masu keta addini a shekarar 2020 saboda bayanan “karya” da ta samu daga wasu ‘yan Najeriya.

Read also

Yan Najeriya sun yi martani kan wata yarinya da ta ci A a darussan WAEC, ta ci 345 a Post UTME

Daraktan MURIC, Ishaq Akintola
Shugaba Buhari bai taba tauyewa 'yan Najeriya 'yancin addini ba, inji MURIC | Hoto: vanguardngr.com
Source: Facebook

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya sanya Rasha, China da wasu kasashe takwas cikin jerin masu keta addini, inda ya cire Najeriya da ke cikin jerin a shekarar 2020.

Blinken, a ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa ya bayyanawa Buhari cewa, an cire Najeriya daga jerin masu take 'yancin addini ne bisa batutuwa na gaskiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni dai ‘yan Najeriya da kungiyoyi da dama da suka hada da kungiyar kiristoci ta Najeriya suka nuna rashin amincewarsu da hakan.

Sun dage cewa har yanzu ana ci gaba da take wa Kiristoci 'yan addini a kasar sakamakon wani shiri na musuluntar da Najeriya.

Sai dai daraktan MURIC ya ce ana kashe Kiristoci da Musulmai a kasar ba tare da duba addini ba.

Read also

Najeriya ba za ta iya juran azabtarwar APC na karin shekaru hudu ba, inji PDP

Yace:

“Muna cikin bala’i da ke fuskantar Kirista da Musulmi gaba daya. Shin gwamnati ce ke kashe Kiristoci? Su wane ne masu kashe Kiristoci a Kudu maso Gabas?
"A yankin Arewa-maso-Gabas inda ake fama da fitina da ‘yan bindiga, masu kashe mutane ba sa nuna wariya; suna kaiwa musulmi da kiristoci hari.
“Najeriya ba ta taba take 'yancin addini ba. Gwamnatin da muke da ita a yanzu ba ta kasance mai take 'yancin addini ba. Gwamnati a matakin tarayya, shugabanmu bai taba samun damar cin zarafin addini ba.

Ya kara da cewa, kawai wasu 'yan Najeriya da ke da ra'ayoyin sukar gwamnati ne ke ganin ana take 'yancin addini.

A bangare guda, wata hukuma a Amurka ta nemi gwamnatin Amurka ta mayar da Najeriya jerin kasashe masu take 'yancin addini, PM News ta ruwaito.

Amurka ta cire Nigeria cikin jerin kasashe masu take 'yancin addini

A wani labarin, kasar Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da ta ce suna take 'yancin masu yin addini a kasashensu, jaridar The Cable ta ruwaito.

Read also

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Amurkan ta saka China, Rasha da wasu kasashe takwas a jerin kasashen da ta ce suna amfani da karfin iko wurin take hakkokin masu addini.

Sakataren Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken 'Religious Freedom Designations'.

Source: Legit.ng News

Online view pixel