Da Ɗuminsa: Amurka Ta Cire Nigeria Cikin Jerin Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini

Da Ɗuminsa: Amurka Ta Cire Nigeria Cikin Jerin Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini

  • Amurka ta cire Nigeria daga jerin kasashen da ta ce suna tauye hakkin masu addini a kasashensu
  • Antony Blinken, Sakataren Amurka ne ya sanar da hakan yayin da ya fitar da jerin kasashen masu tauye yancin addini na 2021
  • Kasashen da ya lissafa a jerin na 2021 sun hada da Saudiyya, Rasha, China, Pakistan, Burma, Turkmenistan da wasu kasashen

Kasar Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da ta ce suna tauye 'yancin masu yin addini a kasashensu, jaridar The Cable ta ruwaito.

Amurkan ta saka China, Rasha da wasu kasashe takwas a jerin kasashen da ta ce suna amfani da karfin iko wurin tauye hakkokin masu addini.

Da Ɗuminsa: Amurka Ta Cire Nigeria Cikin Jerin Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini
Amurka Ta Cire Nigeria Cikin Jerin Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Sakataren Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken 'Religious Freedom Designations'.

Kara karanta wannan

Albashi ba adadi: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da limamin Harami, Sheikh Sudais

A shekarar 2020 ne Amurka ta saka Najeriya da wasu kasashe shida a jerin kasashen da ke tauye hakkin masu addini ko kuma rashin daukan matakan kare masu addinin.

Amma an cire Nigeria cikin jerin kasashen da aka fitar a shekarar 2021.

Blinken, wanda a yanzu yana kasar Kenya da ke Gabashin Afirka don ziyarar aiki, zai karaso Najeriya a wannan makon don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu 'yan fadarsa.

Sakataren na Amurka, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba ya ce:

"Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ta na kare hakkin masu addini a kowanne kasa."

Blinken ya ce gwamnatin Amurka za ta cigaba da saka takunkumi kan kasashe da gwamnatocin da ke hana 'yan kasarsu 'yancin yin addinin da suke so.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Kasashen da Amurka ta lissafa a jerin masu tauye 'yancin addini na 2021

Kasashen da Amurka ta lissafa a matsayin masu tauye 'yan cin addini sun ne:

1. Burma

2. China

3. Eritrea

4. Iran

5. DPRK

6. Pakistan

7. Rasha

8. Saudi Arabia

9. Tajikistan

10. Turkmenistan

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel