Da Duminsa: Fani-Kayode ya yi magana bayan da EFCC ta kama shi kan jabun takardu

Da Duminsa: Fani-Kayode ya yi magana bayan da EFCC ta kama shi kan jabun takardu

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ba ta kama shi ba
  • Fani-Kayode ya ce ya mutunta gayyatar da EFCC ta yi masa sannan ya bar ofishin hukumar da ke Legas da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba
  • Tsohon ministan wanda ya ce jami’an EFCC na da ladabi da kwarewa ya ce an bayar da belinsa ne saboda fahimtarsa

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya musanta cewa hukumar EFCC ta kama shi.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Fani-Kayode a yammacin ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Da Dumi-Dumi: Jami'an hukumar EFCC sun damke Femi Fani-Kayode

An ruwaito cewa an kama Fani-Kayode daga bisani aka kai shi ofishin hukumar ta EFCC na shiyyar Legas bisa zarginsa da yin magudi da kuma buga jabun takardu.

Femi Fani-Kayode
Da Duminsa: Fani-Kayode ya yi magana bayan da EFCC ta kama shi kan jabun takardu | Hoto: dailytrust.com
Source: Twitter

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa a baya an kama tsohon ministan da ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a watan Satumba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a shafinsa na Facebook, Fani-Kayode ya ce hukumar EFCC kawai ta gayyace shi ne, ba ta kama shi ba.

Rubutun ya karanta:

“Na isa otal din George don cin abincin dare, EFCC ba ta taba kama ni ba, an gayyace ni, na tafi zuwa Legas don ganawa dasu, na isa ofishinsu da karfe 2:00 na rana, na bar wurin da karfe 8:30 na dare. An ba da beli na saboda sani na. Sun kasance masu ladabi da kwarewa. Godiya ta tabbata ga Allah."

Read also

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode

A baya kunji cewa, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya shiga hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) a jihar Legas.

Punch ta rahoto cewa tsohon ministan na karkashin binciken hukumar ne bisa zargin amfani da jabun takardu da kuma magudi.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an EFCC sun kai tsohon minista Kayode ofishinsu na jihar Legas ranar Talata.

Source: Legit

Online view pixel