Naira ta gama kumburinta a kasuwar 'yar canji, ta dawo ta kife a kan Dalar Amurka

Naira ta gama kumburinta a kasuwar 'yar canji, ta dawo ta kife a kan Dalar Amurka

  • Darajar Naira ta ragu da kusan N20 tsakanin makon da ya gabata zuwa cikin farkon makon nan
  • Ana canza kowace Dalar Amurka a kan N550, a wasu wuraren kuma har farashin ya haura hakan
  • Amma har yanzu babban bankin Najeriya na CBN ya na saidawa mutane Dalar ne a kan N411.63

Naira ta gagara cigaba da kara daraja a kasuwar canji, inda darajarta ta sullubo a kan Dalar Amurka.

Punch ta fitar da rahoto cewa farashin Dala ya karu a kan Naira a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, 2021.

Hakan na zuwa ne bayan Naira ta yi wasu kwanaki ta na kara daraja a kan kudaden kasashen ketare.

A ranar Alhamis da Juma’ar da suka gabata sai da aka saida Dala tsakanin N535 da N540 a Najeriya.

Read also

Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara idan aka cire tallafi, GMD na NNPC

A halin yanzu farashin Dala ya sake tashi a kasuwar BDC ta ‘yanci kamar yadda rahoton ya bayyana.

Masu harkar canjin kudi sun tabbaarwa jaridar Punch a farkon makon nan cewa Naira ta sauko kadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Naira ta gama kumburinta a kasuwar 'yar canji, ta dawo ta kife a kan Dalar Amurka
Gwamnan CBN Hoto: @Cenbank
Source: Twitter

Naira ta rasa N15 - N20

Ana saida kowace Dalar Amurka daya ne tsakanin N550 da N555. Bambancin ya danganta ne da kasuwa.

Wani wanda ya ke cikin wannan harka ta canji, yace yawan neman Dalan da ake yi ne ya sa ta kara tsada.

Economic Confidential tace a kafar babban bankin Najeriya na CBN, Naira ta rage daraja da 0.16%.

Hakan ya na nufin an aba masu shigo da kaya da kasashen waje Dala $1 a kan N415.07 a makon nan.

Amma duk da haka bankin na CBN bai canza farashin Dala a shafinsa ba, ya na nuna cewa ta na nan a N411.63.

Read also

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

Shugaban kasan da ya dace da Najeriya

A ranar Litinin gwamna Aminu Tambuwal ya bada shawara game da irin shugaban da ya kamata a zaba.

Aminu Tambuwal yace ba a bukatar shugaban da zai nuna bambancin addini ko kabilanci a mulkinsa.

Source: Legit

Online view pixel