An yi jana’izar Jigon jam’iyyar APC da yan bindiga suka kashe a hanyar Kaduna/Abuja

An yi jana’izar Jigon jam’iyyar APC da yan bindiga suka kashe a hanyar Kaduna/Abuja

  • Manyan jiga-jigan siyasa sun halarci Sallar Jana'izar tsohon dan takaran gwamnan jihar Zamfara
  • Babban jigon APCn ya rasa ransa ne hannun yan bindiga yayinda suka yi kokarin garkuwa da shi
  • Dimbin jama'a sun shaida wannan Sallah da akayi a Masallacin Annur dake Unguwar Wuse Abuja

Abuja - An yi jana'izar tsohon dan takaran kujeran gwamnan jihar Zamfara karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Sagir Hamidu, wanda aka kashe ranar Lahadi.

An kashe Sagir Hamidu, wanda babba jigon APC, a babban titin Kaduna/Abuja lokacin da yan bindiga suka bude masa wuta.

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izarsa akwai Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle; tsohon Gwamnan jihar, AbdulAziz Yari.

Hotuna daga shafukan Hamdan Alhazzai Shinkafi sun nuna yadda sallar jana'izar ta gudana.

Read also

APC ta ba Buhari wuka da nama na tsayar da lokacin gudanar taron gangami

A jawabinsa, ya bayyana cewa jana'izar ta gudana ne a birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, an gabatar da Sallar jana'izarsa a masallacin ANNUR Dake Wuse 2 A Abuja. Jim kadan bayan kammala sallar AZZAHAR(ZUHR) a yau duk acikin garin na Abuja babban birnin tarayyar Nigeria.

An yi jana’iza
An yi jana’izar Jigon jam’iyyar APC da yan bindiga suka kashe a hanyar Kaduna/Abuja Hoto: Hamdan Alhazzai
Source: Facebook

Yace:

"Marigayin wanda yassamu shaidu ga Al'ummar musulmi Dadama wajan gudanar da zumunchi da son juna dakuma kyautata mu'amula da kafatanin al'ummar musulmi.
Dattawan jihar Zamfara a karkashin Jagorancin Mai girma Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Jagoran Jam’iyyar APC Hon Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara), Hon.Lawal M.Liman (Gabdon Kaura) Shugaban Riko na Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, Sen.Kabiru Garba Marafa,CON. (Marafan Gusau), H'E Dr.Dauda Lawan Dare (Gamjin Gusau), Hon.Ikira Aliyu Bilbis
Muna Adduar Allah Yaji Kansa Ya Gafartamasa ya ƙarɓi baƙuncinta yakuma albarkaci bayansa amin."

Read also

Hotuna: Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

Marigayin wadda yakeda shekaru sittin da ukku(63) a duniya yatafi yabar mata ɗaya (01) da ƴaƴa Ashirin da ɗaya (21) da Yan uwa da abokanan Arziki.

Source: Legit

Online view pixel