Shekaru 19 kenan a bakin aikin nan, ina jin dadinta sosai: Jami'in Yellow Fiba a Legas

Shekaru 19 kenan a bakin aikin nan, ina jin dadinta sosai: Jami'in Yellow Fiba a Legas

  • Adefolalu Timothy Olusegun jami'in LASTMA ne a jihar Legas wanda ya shahara da rawa yayinda yake baiwa motoci hannu
  • Jami'i wanda ya shiga aikin tun shekarar 2002 ya ce ba karamin son aikinsa yake yi ba kuma bai jin dadi idan bai yi ba
  • Timothy wanda yayi aikin daukan hoto kafin samun wannan aiki, yaje kawai yana farin cikin baiwa motoci hannu a Legas

Adefolalu Timothy Olusegun jami'in hukumar takaita cakudaidainiyar ababen hawa a Legas watau LASTMA kuma kuma ya zama shahrarre bisa salon da yake tafiyar da aikinsa.

Adefolalu ya shahara da rawa a tsakiyan titi yayinda yake aikinsa.

Shekatunsa 19 kenan a bakin aiki

A hirarsa da BBC News Pidgin, Timothy yace ya shiga aikin LASTMA ne a shekarar 2002 bayan kwashe shekaru biyar yana aikin daukan hoto.

Read also

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Mutumin ya bayyana cewa yana matukar jin dadin aikinsa kuma duk ranar da bai yi ba, ba ya jin dadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'in Yellow Fiba a Legas
Shekaru 19 kenan a bakin aikin nan, ina jin dadinta sosai: Jami'in Yellow Fiba a Legas Hoto: BBC Pidgin
Source: Facebook

Rayuwa a matsayin jami'in LASTMA

Timothy ya bayyana cewa aikinsa na rage cakudaidainiyar motoci a Legas kuma mutane na jin dadin aikinsa.

Yace mutane na son sa sosai da abin ya kai idan ba shi ke bakin titi ba, abokan aikinsa na shan suka.

Yace duk da kokarin da sukeyi bakin aiki, wasu direbobi sai sun yi yunkurin saba doka.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel