Katsina: ‘Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta

Katsina: ‘Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta

  • ‘Yan bindiga sun halaka ‘yan sanda 2 sakamakon wata musayar wuta da su ka yi a ranar Alhamis kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sanusi Buba ya shaida
  • Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar inda ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Safana
  • Kwamishinan ya ce hakan ya auku ne yayin dawata runduna wacce mataimakinsa, Aminu Umar ya jagoranta su ka halaka ‘yan bindiga 2 sannan su ka kwato makamai da dama daga hannunsu

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta rasa jami’anta biyu yayin musayar wuta da ‘yan bindiga a ranar Alhamis kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sanusi Buba ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Katsina.

Read also

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Togan

Buba ya ce cikin ‘yan sandan da su ka rasa rayukansu akwai wani ASP Yakubu Joshua da ke aiki da 27 Police Mobile Force (PMF) Katsina da Sajan Zaharadeen Yuguda da ke aiki a Safana.

Katsina: ‘Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta
'Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta a Katsina. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

A cewarsa hakan ya biyo bayan bude wutar da su ka yi wa maboyar ‘yan bindiga da ke kauyen Baure a karamar hukumar Safana da ke jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai CP Buba ya ce rundunar ‘yan sanda wacce mataimakin kwamishinan, ACO Aminu Umar ya jagoranta ta samu nasarar ragargazar ‘yan bindigan inda su ka halaka 2 daga cikinsu.

Yayin yi musu aman wutar sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK 37 da sauran miyagun makamai da ga wurinsu, Daily Trust ta rawaito..

Sun kwace babura marasa rijista

Kamar yadda takardar ta bayyana:

“A ranar 18 ga watan Nuwamban 2021 da misalin karfe 5 na yamma, kamar yadda jami’an bincike na sirri suka tabbatar, ACP Aminu Umar ya jagoranci rundunar ‘yan sanda da ‘yan sa kai zuwa maboyar ‘yan bindiga a kauyen Baure da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina don ragargazarsu.”

Read also

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Ya kara da bayyana yadda su ka samu nasarar amshe wasu babura marasa rijista da wata rigar layu daga hannunsu.

A cewarsa:

“Sai dai yayin musayar wutar, jaruman jami’ai 2, AP.NO.151332 Asp Yakubu Joshua na 27 PMF, Katsina da F/NO.264575 Sgt Zaharadeen Yuguda na ofishin Safana sun rasa rayukansu.”

Ya kamata jama’a su ba hukuma hadin kai

Ya bukaci jama’an gari da su hada kai da jami’an tsaro wurin samar da labarai masu amfani don kawar da ‘yan bindiga da masu taimakonsu.

Ya kara da tabbatar wa jama’a da cewa ‘yan sanda su na iyakar kokarinsu na ganin sun kawo karshen ta’addanci da kuma gabatar da duk wani mai laifi gaban hukuma don ya dandana kudarsa.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Read also

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Source: Legit.ng

Online view pixel