Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Togan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Togan

  • A kalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani farmaki da ‘yan bindiga su ka kai garin Tor-Togan a ranar Alhamis
  • Sun raunana mutane da dama yayin da su ka kai harin da misalin karfe 5pm kamar yadda shugaban karamar hukumar Katsina Ala, Hon. Alfled Atera ya tabbatar
  • Tor Tongo gari ne na manoma da ke kan babban titin gwamnatin tarayya a mazabar Binuwai ta arewa maso gabas kuma yawancin wadanda su ka halaka ‘yan sa kai ne

Jihar Benue - A kalla mutane bakwai ne aka tabbatar yan bindiga sun kashe a harin da suka kai garin Tor-Togan a daren ranar Alhamis kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wasu da dama sun jikkata sakamakon harin da aka kai misalin karfe 5.30 na yammaci.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gagarumar gobarar gas ta hargitsa garin Ibadan

Shugaban karamar hukumar Katsina Ala, Hon. Alfled Atere ya tabbatar da afkuwar harin.

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Torgan
Da Duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Torgan
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tor-Tongo wani gari ne na manoma a kan hanyar Katsina Ala - Takum a yankin arewa maso gabashin Benue.

Arera ya shaidawa manema labarai cewa mafi yawancin wadanda aka kashe jami'an sa kai ne na CVG.

Ya ce wasu mutane biyar sun jikkata cikinsu, har da wani fasto wanda aka harba kafin su tsere.

Ya yi ikirarin cewa yan bindigan mambobin kungiyar tsohon shugaban yan daba mai suna Azonto ne.

Azonto ya na hannun jami’an tsaron jihar Taraba tun watan da ya gabata.

A cewarsa ‘yan sa kan CVG ba su da wasu makamai, shiyasa ba sa iya yin wani kokari wurin dakatar da hare-hare.

Wani jami’in soji wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

Ya ce:

“A ranar Alhamis da misalin 4:44 na dare a garin Tor Torga da ke karkashin karamar hukumar Katsina Ala, ‘yan bindiga su ka kutso kawanansu ta madakatar ‘yan sa kai.
“An yi gaggawar sanar da rundunar Operation Whirl Stroke, OPWS wadanda su ka yi gaggawar zuwa wurin sannan su ka bi bayan ‘yan bindigan amma ba su gansu ba.
“Sai dai sun ga gawawwaki 7 da kuma mutane 3 da su ka samu miyagun raunuka kuma yanzu haka su na asibiti ana duba laifyarsu.”

Sai dai wani mazaunin Tor Tongo, Terseer Jato, da ya ke bayani ya musanta batun yadda rundunar Operation Whirl Stroke tace ta bi bayan ‘yan bindigan.

A cewarsa an sanar da sojojin halin da ake ciki amma babu wani abu da su ka yi sai da aka halaka mutane 9.

Ya zargi jami’an Operation Whirl Stroke da kin yin ayyukan da ya kamata tun bayan kwamandansu Manjo Janar Yekini ya tafi.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Ya bayyana cewa ‘yan bindiga su na zuwa su ci karensu babu babbaka a Katsina Ala.

Ya yi kira ga sojoji akan dagewa wurin yin ayyukansu da kuma kulawa da rayuka da dukiyoyin al’umma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel