Ko kwana guda ba zan nemi kari ba idan wa'adi na ya kare: Buhari ga Sakataren Amurka

Ko kwana guda ba zan nemi kari ba idan wa'adi na ya kare: Buhari ga Sakataren Amurka

  • Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da Buhari a Aso Rock Villa Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa ba zai nemi tazarce ba idan wa'adinsa ya kare a Mayun 2023
  • Shugaban kasan ya sake bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin sakataren wajen Amurka, Anthony Blinken
  • Wasu mawaka, yan siyasa kuma masoya Buhari sun yi kira gareshi ya cigaba da mulki ko wa'adinsa ya kare

Aso Rock - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ko kwana guda ba zai nemi kari ba idan wa'adin mulkin ya kare ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Sakataren Wajen Amurka, Anthony Blinken, a fadarsa ta Aso Rock Villa a Abuja.

Buhari ya bayyanawa Blinken cewa wadanda suka yi yunkurin haka a baya sun ji kunya.

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya aikewa Legit.ng.

A jawabin, ya nakalto Buhari da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wadanda suka yi yunkurin haka sun ji kunya, kuma sun kunyata. Mutum ma yayi sa'an samun wa'adi biyu."
"Wasu sun yi kokarin haka basu samu ba. Yan Najeriya sun amince salon gwamnatin Amurka shine mafi kyau."

Buhari da Sakataren Amurka
Ko kwana guda ba zan nemi kari ba idan wa'adi na ya kare: Buhari ga Sakataren Amurka Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da Buhari a Aso Rock Villa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Blinken ya isa fadar Aso Rock Villa ne da misalin karfe 3:47 na rana, kuma babban jami’in hulda da jama’a na kasa (SCOP), Ambasada Lawal Kazaure, wanda ya kai shi ofishin shugaban kasar ne ya tarbe shi.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Bayan ganawar da Buhari, sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka zai zarce zuwa ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo inda zasu rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin Najeriya da kasar Amurka.

Bayan haka kuma zai yi taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, kafin ya bar fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel