An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba

An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba

  • An samu rahotanni akan yadda wajibi ne a jinkirta kai gawa daga wata kasar zuwa wata sakamakon wasu takardu da za a cika
  • Majiyoyi sun bayyana yadda ake kyautata zaton gawar Sani Dangote za ta iso Najeriya ranar Laraba maimakon yadda ake tunanin isowarta ranar Talata
  • Wata majiya ta bayyana yadda aka taho da gawar mamacin daga Amurka kuma ana kyautata zaton za ta iso Najeriya da safiyar Laraba

Gawar marigayi Sani Dangote ba ta iso daga Amurka ba har a yammcin Talata sakamakon wasu cike-ciken takardu da ba a yi ba.

Wata majiya daga iyalan ta sanar da Daily Trust cewa ana tsammanin za a kawo gawar Kano a ranar Laraba.

An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba
An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

An samu bayanai akan yadda lokaci ya tafi ba a taho da gawar Sani Dangote ba, kanin attajiri Aliko Dangote, sakamakon wasu takardu da ake ta cikewa.

Kara karanta wannan

Gawar Sani Dangote za ta iso Kano daga Amurka a yau Talata domin jana'iza

Kowa ya san yadda yanayin tafiya da gawa daga kasa zuwa kasa ya ke zama abu mai wahalar gaske.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi sun kara da bayyana yadda ake kyautata zaton gawar Marigayi Sani za ta iso Najeriya ranar Laraba da yamma maimakon ranar Talata da ake tunanin isowarta.

“Muna ji daga wurinsu lokaci bayan lokaci,cika takardu ne su ke ya janyo daukar lokaci kafin a iso Najeriya da gawar tun daga Amurka.
“Sakamakon daukar lokacin, muna kyautata zaton za su iso Najeriya ranar Laraba da safe don a yi jana’iza. Kuma za a sanar da lokacin jana’iza da zarar sun iso,” a cewar majiyar.

Wata majiya daga ‘yan uwan mamacin ta sanar da Daily Trust cewa, gawar mamacin ta baro Amurka, kuma za ta iso Najeriya ranar Laraba kasar Najeriya.

Mamacin kani ne ga attajirin mai kudin Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara

Ya rasu ne a Amurka a wani asibiti, ranar 14 ga watan Nuwamban 2021 yana da shekaru 61.

Gawar Sani Dangote za ta iso Kano daga Amurka a yau Talata domin jana'iza

A wani labari na daban, a yau Talata ake sa ran gawar Sani Dangote, kanin mashahurin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, za ta iso Najeriya daga kasar Amurka inda ya rasu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sani shi ne mataimakin shugaban kamfanonin Dangote kuma ya rasu a ranar Lahadi a Amurka bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Wata majiya makusanciya ga iyalan ta ce, "Sani Dangote tuni dama ya ke fama da sankarar hanji kuma ya tafi Amurka domin samun magani, amma kamar yadda Allah ya so, ya rasu ya na da shekaru 61."

Asali: Legit.ng

Online view pixel