Dala tayi mummunan fadin da ta rasa N50 a ‘yan kwanaki, $1 ta koma N525 daga N575

Dala tayi mummunan fadin da ta rasa N50 a ‘yan kwanaki, $1 ta koma N525 daga N575

  • A ‘yan kwanakin baya-bayan nan, babu abin da Naira take yi sai kara daraja a kasuwar canji na BDC
  • Kudin Najeriyar ya kara daraja a kan Dala bayan Naira ta gangara zuwa N575 a kan kowace fam $1
  • Abin da ake canza kowace fam $1 a kasuwar canji yanzu ya koma N525, Dalar Amurka ta rasa N50

Nigeria - Naira ta dauki lokaci mai tsawo tana farfadowa a kasuwar canji, inda ta kara daraja da N25 tun bayan ta kife zuwa N575 a karshen watan Satumba.

Wani rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, 2021, ya bayyana cewa kudin Najeriyan ya karu da akalla N25 kan Dalar Amurka.

‘Yan jarida sun zagaya kasuwar canji watau Bureau De Change (BDC) na unguwar Wuse a garin Abuja, inda suka ga cewa Dalar Amurka tana kara rage tsada.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa

Bayan babban bankin CBN ya daina ba ‘yan kasuwar canji Dala, Naira ta fadi war-was a kasuwa tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, har sai da $1 ta kai N575.

Naira ta rage daraja da N85 bayan faduwarta daga N490 zuwa N575. Sahelian Times ta bayyana cewa yanzu lamarin ya canza, Dalar ce ta ke karyewa a kasuwa.

BDC Operators
'Yan canjin Dala Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan kasuwa suna kukan rashin cinikin Dala

Wani ‘dan kasuwar canji ya shaidawa manema labarai cewa Naira tana ta yin daraja a kasuwannin canji, kuma su kansu ba su san dalilin hakan ba.

“Ban ma san me yake faruwa ba. Ina da Dala da yawa, amma babu wasu masu saye. Naira tana kara daraja a kullum.” - Wani ‘Dan kasuwar canji.

Kwararren ma’aikacin banki ya bayyana dalilin tashin Naira

Wani masanin tattalin arziki, Paul Alaje, ya ji dadin farfadowar da Naira take yi, yace nan da karshen shekara, babu mamaki Dala ta karye, ta koma kusan N500.

Kara karanta wannan

COVID-19: Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 9.9 a kan wanke hannu a 2021

Alaje yace babu dalilin da zai sa CBN ta karya darajar Naira a yanzu saboda gudun tayi raga-raga.

Farfesa Uche Uwaleke yace kumburar asusun kudin waje ya jawo Naira ta tashi. Sannan Dala za ta kara yin kasa domin za ayi ta aiko kudi Najeriya nan da kirismeti.

Lokaci da £1 ta kai har N780.

A ranar Litinin, 20 a watan Satumba, 2021 aka ji cewa farashin dala ya koma tsakanin N572 zuwa N575 a hannun ‘yan canji bayan CBN ya dakatar da aikin Aboki Fx.

A wancan lokaci, a kasuwannin BDC na Kano, farashin Dalar Amurka ya kai N575. Naira ta kuma rasa kimar ta a kan Pound Sterling, inda duk fam £1 ta kai har N780.

Asali: Legit.ng

Online view pixel