A shekara 74, Atiku Abubakar ya gama karatun digirin 'Masters' a Jami’ar Kasar Birtaniya

A shekara 74, Atiku Abubakar ya gama karatun digirin 'Masters' a Jami’ar Kasar Birtaniya

  • Shekaru sama da 50 da yin difloma, Atiku Abubakar ya kammala karatun digirgir a kasar Birtaniya
  • Wazirin Adamawa ya yi digiri ne a ilmin huldatayar kasashe a jami’ar Anglia Ruskin da ke Ingila
  • Shugaban babban bankin AfDB ya bayyana wannan da yake taya Atiku murna a Twitter kwanaki

Abidjan - Shugaban babban bankin cigaban Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina, ya dauki lokacinsa, ya taya Alhaji Atiku Abubakar murnar kammala karatu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya gama karatun digirgir ne a jami’ar nan ta Anglia Ruskin da ke birnin Cambrige, a kasar Birtaniya.

Dr. Akinwumi Adesina wanda ya taba yin Ministan harkar gona, ya yi amfani da shafinsa na Twitter a karshen makon da ya wuce, ya taya Atiku murna.

A sakon taya murnar da Dr. Akinwumi Adesina ya fitar a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2021, yace Atiku Abubakar abin koyi ne ga sauran jama’a, ya jinjina masa.

Read also

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

Daga bayanin tsohon Ministan na Najeriya, za a fahimci cewa tun a makon jiya, Atiku ya gama karatun na sa a wannan jami’a da ta fi shekara 160 da kafuwa.

Atiku Abubakar
Atiku da Adesina da kayan jami'a Hoto: @akin_adesina
Source: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Akinwumi Adesina ya yabawa Atiku Abubakar

“Ina taya Mai girma Atiku Abubakar @atiku, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a kan kammala digirinsa a harkar ilmin huldar kasashe a jami’ar Anglia Ruskin University, Cambridge, UK.”
“Maida hankalinka da kwazonka a kan harkar ilmi zai zaburar da wasu. Sannu da kokari, ran ka ya dade.” – Dr. Akinwumi Adesina.

Gemu ba ya hana karatu

A tsakiyar shekarar nan ne aka ji cewa ‘dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar adawa a zaben 2019, yana karatun digirgir a jami’ar ta Anglia Ruskin a kasar Ingila.

Duk da shekarunsa, wannan bai hana ‘dan siyasar komawa makaranta ba. Wasu suna ganin ilmin zai karfafa masa idan ya sake fitowa neman takara a Najeriya.

Read also

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

Jaridar The Cable tace a shekarar 1967 ne Atiku Abubakar ya yi difloma a makarantar kula da tsabta a Kano, daga baya ya yi difloma a ilmin shari’a a ABU Zaria.

Wannan ne karon farko da babban 'dan siyasar zai samu shaidar karatun digiri a rayuwarsa.

Malala Yousafzai ta zama amarya

A makon jiya ne aka ji ‘Yar gwagwarmayar nan da take kare hakkin mata, Malala Yousafzai, ta saki layi daga adawa ga aure, tace ta gane dawar garin a dakin miji.

Malala wanda ta taba cewa ba ta ga dalilin yin aure ba, ta fito yanzu tana cewa ba ta adawa da aure, sai dai ta damu ne da yadda ake wahalar da mata a gidan aure.

Source: Legit.ng

Online view pixel