Sai yanzu na fahimci menene aure, bayan na shiga daga ciki inji Malala Yousafzai

Sai yanzu na fahimci menene aure, bayan na shiga daga ciki inji Malala Yousafzai

  • Malala Yousafzai ta yi aure duk da an taba ji tana ta kushe tsarin rayuwar aure a shekarun baya
  • Amaryar tace yanzu ne ta fahimci aure, bayan ta tare da sahibinta Asser Mlik a cikin makon jiya
  • Malala tace sam ba ta adawa da aure, sai dai tana sukar zaluncin da ake yi wa kananan mata ne

England - Bayan kwanaki kadan da auren sahibinta, shahararriyar ‘yar gwagwarmayar nan, Malala Yousafzai, ta saki layin da ta ke kai a kan ra’ayin aure.

Malala Yousafzai wanda ta taba lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya a Duniya, ta yarda tayi wa aure mummunar fahimtar da yanzu take gane gaskiyar lamarin.

Yousafzai mai shekaru 24 a Duniya, ta zanta da BBC, inda ta amsa tambaya a kan yadda aka ji ta canza ra’ayin ta a game da zaman aure, bayan tayi aure kwanan nan.

Read also

SSS sun kame matashin da ya zolayi Zainab Nasir kan auren 'yar gwagwarmaya Malala

Rahoton yace ‘Dan jaridar ya fara tattaunawa da ‘yar gwagwarmayar ne bayan ya yi mata murnar aurenta da Mista Asser Mlik da aka yi a makon da ya gabata.

Matashiyar tayi karin haske, tace matsalar ta da aure a lokacin, shi ne yadda ake yi wa wasu auren wuri da irin halin da kananan mata ke shiga a gidan miji.

Malala Yousafzai
Malala Yousafzai da Asser Mlik Hoto: MaLIN FEHEZAI
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''Ba na adawa da aure, na dai damu ne da yadda ake yin auren, da abin da yara mata da aka yi wa aure a kananan shekaru suke fuskanta.” - Malala.

Malala Yousafzai ta cigaba

“Da auren dole, da halin da suke fuskanta bayan mutuwar auren, da kuma rashin daidaito tsakanin miji da mata na matukar daga min hankali.”

Amaryar ta kuma shaidawa manema labarai cewa al’ada tana taka mummunar rawa a kan yadda al’umma suka dauki aure, hakan ya sa ta fito tana sukar tsarin.

Read also

Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55

Ni na yi sa’ar auren Asser Mlik

Duk da matsalolin da suke tattare da wasu auren, Malala Yousafzai tace ta yi dacen miji, domin ya fahimci dalilin da ya sa take fafatuka domin ta kare ‘yan mata.

Mlik ya kyale wannan Baiwar Allah ta cigaba da aikin da aka san ta da shi na fafatukar nemawa ‘yan mata ‘yanci, tare da yunkurin ba su kariya a fadin Duniya.

Zabe a kasar Libya

A karshen shekarar bana ake sa ran ayi zaben Shugabann kasa a Libya. Legit.ng ta fahimci cewa amma dai babu tabbacin cewa za a gudanar da zaben a Disamba.

Yaron tsohon shugaban kasa Muammar Gaddafi, Saif Al-Islam zai gwabza da irinsu Firayim Minista, Hamid Dbeibah da Khalifa Haftar a zaben shekarar nan.

Source: Legit

Online view pixel