Sanusi, Sultan Dasuki da Sarakuna 5 da suka rasa rawaninsu a dalilin sabani da gwamnati

Sanusi, Sultan Dasuki da Sarakuna 5 da suka rasa rawaninsu a dalilin sabani da gwamnati

  • Nigeria - Ba bakon abu ba ne gwamnati ta tsige Sarki a Najeriya. An ga irin wannan tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo, kuma yana faruwa har gobe.
  • A yankin kudancin Najeriya an yi Sarakuna a jihohin Oyo da Ribas da suka rasa mukamansu a ‘yan shekarun bayan nan, a dalilin rigimarsu da gwamnonin jiharsu.
  • A shekarun baya kuwa, an tsige irinsu Sarkin Owo, Olateru Olagbegi, Ibikunle Akitoye wanda ya mulki kasar Legas, da Dejin Akure, Mai martaba Oluwadare Adesina.

Wannan karo Legit.ng Hausa ta kai ga sarakuna masu karfi da aka tunbuke a Arewacin Najeriya.

Su wanene Sarakunan da aka tsige?

1. Umaru Tukur

Na farko a jerin na mu shi ne Sarkin Muri na 11, Umaru Tukur wanda gwamnan Gongola, Yohana Madaki ya tunbuke bayan ya yi shekara 20 yana mulki a 1986, aka batar da shi a kasar Mubi.

Read also

Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

2. Abubakar Dallaje

Abubakar Dallaje na kasar Katsina yana daga cikin sarakunan da suka rasa rawaninsu bayan zuwan Turawa. Gwamna Fredrick Lugard ya tsige shi ne a 1906, ya nada Sarki Muhammadu Dikko.

Sanusi
Muhammadu Sanusi II Hoto: @Majeeda
Source: Instagram

3. Alu Dansidi

Malam Alu Dansidi ya gamu da fushin Turawan mulkin mallaka bayan ya shekara kusan 20 yana mulkin kasar Zazzau, An tsige jikan na Malam Musa Bamalli ne yana da shekara 83 a Duniya.

4. Mustapha Jokolo

Mustapha Jokolo yana cikin fitattun Sarakunan da aka tunbuke. A 1995 ya zama Sarkin Gwandu, daga baya gwamnatin Adamu Aleiro ta sauke shi, ta tura shi garin Obi, a kasar Nasarawa.

Sarakunan Kano biyu sun rasa rawani a shekara 57

5. Muhammad Sanusi I

Bayan mutuwar Abdullahi Bayero Muhammadu Sanusi I ya zama Sarki. Amma a 1963, gwamnan Arewa, Kashim Ibrahim ya tursasa masa ya yi murabus. Daga nan ya koma Azare da zama.

Read also

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

6. Muhammad Sanusi II

Jikan Sanusi I watau Muhammadu Sanusi II ya hau mulki a 2014, shi ma ya rasa rawaninsa a 2020. A karshe Gwamna Abdullahi Ganduje ya sauke shi bayan kirkiro wasu masarautu a Kano.

7. Sultan Ibrahim Dasuki

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Ibrahim Dasuki ya bar kujerar Sultan ne a 1996, bayan gwamnatin Yakubu Muzu ta zarge shi da rashin kunya. Marigayi Mohammed Maccido ne ya gaje shi.

Sarakuna 7 sun kwanta dama a Arewa

Idan ba ku manta ba, kwanakin baya mun kawo maku jerin wasu shahararrun Sarakunan kasar Arewacin Najeriya 7 da suka rasu a cikin shekara dayan da ta wuce.

A shekarar 2020 Sarakunan kasar Zazzau da Rano suka rasu. Sannan a shekarar nan aka rasa Sarakuna biyu a Neja, baya ga Sarkin Gaya da ya cika kwanan nan.

Source: Legit.ng

Online view pixel