Jerin fitattun Sarakunan Arewacin Najeriya 7 da suka rasu a cikin shekara daya

Jerin fitattun Sarakunan Arewacin Najeriya 7 da suka rasu a cikin shekara daya

  • Yanzu haka ana makokin Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim AbdulKadir
  • A cikin shekarar 2020 Sarakunan kasar Zazzau da Rano suka rasu
  • Har ila yau a shekarar nan aka rasa manyan Sarakuna biyu a Neja

1. Sarkin Zazzau

Na farko a jerin na mu shi ne Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu yana da shekaru 84 a Duniya. Marigayin ya yi mulki a kasar Zazzau na shekaru 45.

A Satumban nan aka cika shekara daya da rasuwar daya daga cikin sarakunan da suka dade a mulki.

2. Sarkin Kontagora

A farkon watan nan aka samu labarin mutuwar Mai martaba Sarkin Kontagora. Alhaji Saidu Umaru Namaska ya rasu bayan shekaru 48 yana sarauta.

Har zuwa yanzu dai gwamnatin jihar Neja ba ta kai ga nada wanda zai maye gurbin Mai Sudan ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara

3. Sarkin Rano

A shekarar 2020 ne mutanen kasar Rano suka wayi gari da labarin mutuwar Sarkinsu, Mai martaba Abubakar-Ila wanda ya mutu yana da shekara 74.

Shehu Idris
Marigayi Sarki Shehu Idris Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

4. Sarkin Kagara

Har ila yau a shekarar nan ne Mai martaba Sarkin Karaga a jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko ya rasu. An ji cewa Sarkin ya bar Duniya ne yana da shekaru 91.

5. Sarkin Lere

Kafin watan azumin wannan shekarar ne aka tabbatar da mutuwar Mai martaba Sarkin Lere, Birgediya Janar Abubakar Garba Mohammed (mai ritaya).

6. Sarkin Chikun

Har ila yau a jihar ta Kaduna an rasa Mai martaba Esu Chikun, Dr Danjuma Barde. Basaraken ya rasu ne a asibitin sojojin kasa na 44 da ke garin Kaduna.

7. Sarkin Gaya

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya aika wa 'Yan Majalisa takarda, ya yi sababbin nadin mukamai a EFCC

Na karshe a jerin na mu shi ne Sarkin Gaya wanda a yau Laraba, 22 ga Satumba 2021, Allah ya yi wa Mai Martaba Alhaji Ibrahim AbdulKadir din rasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng