Yadda mutanen gari suke biyan ‘zakkah’ ga ‘Yan ta’addan Boko Haram salin-alin a jihar Borno

Yadda mutanen gari suke biyan ‘zakkah’ ga ‘Yan ta’addan Boko Haram salin-alin a jihar Borno

  • A yankin Damboa a jihar Borno, mutane suna biyan haraji ga Islamic State of West Africa Province.
  • Sojojin Islamic State of West Africa Province suna karbar dukiyar manoma a matsayin zakkarsu.
  • Haka zalika direbobi suna biyan kudin bin titi domin su samu damar yin harkokinsu salin-alin.

Borno - Mazauna da manoman garin Damboa a jihar Borno sun soma biyan haraji da sunan zakkah ga ‘yan ta’addan Islamic State of West Africa Province.

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa kungiyar Islamic State of West Africa Province ta na karbar wadannan kudi ga mutanen da ke karkashin inda take iko.

A addinin musulunci, masu dukiya suna cire wani kaso daga cikin arzikinsu na kudi da amfanin gona duk shekara, su ba mabukata domin rage talauci a al’umma.

Read also

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

Wani babban jami’in gwamnati ya shaidawa Daily Trust cewa a halin yanzu, manoma da-dama suna karkashin ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP a garin na Damboa.

Mutane ba su son gwamnati ta sani

“’yan ta’addan suna kyale mazauna yankin su yi noma, sai su karbi abin da suka kira haraji (kudin da ake ba mabukata duk shekara).”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Suna karbar wannan daga hannun kowane manomi bayan ya samu amfanin gona.” - Jami’in.
‘Yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno
Wasu mayakan ISWAP Hoto: www.theportal-center.com
Source: UGC

Majiyar tace babu wani manomi da ya isa ya kauracewa wannan tsari da ‘yan ta’addan suka shigo da shi. Dole kowa ya bada wani kaso daga abin da ya noma.

Wani manomi mai suna Musa Mrusha da ya zanta da ’yan jarida, ya bayyana cewa mutanen da aka tursasawa biyan wannan zakkah, ba su so hukuma ta san batun.

“A lokutan baya, mayakan Boko Haram sun kashe mutane rututu a lokacin girbin gona. Shin a wannan shekarar ka ji irin wannan labarin?” - Musa Mrusha.

Read also

Kano: Jami’an SSS sun bankaɗo ‘yan fashin da ke bin sahun mutane daga banki har zuwa gidansu

Direbobi suna biyan kudi domin su bi hanyoyi lafiya kalau

A farkon bara, ‘Yan IPOB suka zo gonar Mrusha, suka ce masa idan ya cire amfanin gona zai bada wani abu, ya kuma amince da wannan tsari hankalinsa a kwance.

Akasin yadda aka san mayakan Shekau da kashe mutane, 'yan ISWAP suna sa kayan sojoji, su karbi harajin hanya daga hannun direbobi da ke bin titunan Damboa.

Masu tada kayar baya

Lauyoyi irisu Femi Falana SAN sun bukaci a gaggauta samun mafita a kan tirka-tikar kungiyar IPOB, Kanu da Sunday Igboho da suke da ra'ayin a barka Najeriya.

Manyan Lauyoyi sun bada shawarar cewa idan har za a sasanta da Nnamdi Kanu da Sunday Igboho a wajen kotu, to gwamnati tayi maza wajen samu matsaya.

Source: Legit.ng

Online view pixel