Manyan Lauyoyi sun ba Gwamnati shawarar yadda za a zauna lafiya da Nnamdi Kanu da Igboho

Manyan Lauyoyi sun ba Gwamnati shawarar yadda za a zauna lafiya da Nnamdi Kanu da Igboho

  • Wasu manyan kauyoyi sun tofa albarkacin bakinsu a kan kiraye-kirayen da ake yi na a raba Najeriya.
  • Femi Falana da wasu kwararrun lauyoyi sun ba gwamnati shawara ta zauna da masu wannan ra’ayin.
  • A cewar lauyoyin, shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya magance matsalar da yin karfa-karfa ba.

Abuja - Wasu daga cikin manyan lauyoyin Najeriya sun tofa albarkacinsu game da barazanar da gwamnati take fuskanta daga masu neman a barka kasa.

Punch ta yi hira da kwararrun lauyoyi uku wadanda suka kai matsayin SAN, bayan gwamnatin tarayya ta nuna yiwuwar ta zauna da wadannan mutane.

Femi Falana, Ebun-Olu Adegboruwa, da Ifedayo Adedipe sun yi kira ga gwamnati ta yi maza ya fara shirin sulhu da manyan masu kiran a barka Najeriya.

A hirarrakin da lauyoyin suka yi da manema labarai, sun nuna rashin jin dadinsu a kan yadda aka tsare Sunday Adeyemo da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Menene ra'ayin kwararrun masanan shari'a?

Femi Falana yace babu yadda gwamnatin tarayya ta iya, dole ne tayi amfani da hanyar siyasa, ta shawo kan wadannan matsaloli da ake fama da su a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mutane da dama sun nemi ayi sulhu (ta siyasa), kuma dole gwamnati ta gaggauta yin wannan domin ba yadda ta iya, don karfi ba zai yi aiki ba.”
Buhari
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: www.aljazeera.com
Asali: UGC

“Wannan ba yakin makami ba ne, yaki ne na akida. Idan matasa suka ce; ‘mun gaji da yadda ake mulki, muna so mu balle’. Sai gwamnati ta shawo kansu.”
“Yadda za a ci wannan yaki kawai shi ne a tabbatar za ayi wa kowa adalci a kasar nan.” – Falana.

Shi kuma Ebun-Olu Adegboruwa SAN yana ganin ya kamata tun farko a rika zama da masu neman a balle, a maimakon a rika yi masu kallon ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

“Zan ce an makara bayan gwamnati ta damke shugabannin wadanan tafiya. Ya kamata a a fara da sulhu ne, idan ya ki, sai a nemi wata mafitar.” – Adegboruwa.

Shi ma Ifedayo Adedipe yace sasantawa ya kamata ayi da wadannan mutane kamar yadda gwamnatocin Obasanjo da ‘Yar’adua suka yi, aka samu zaman lafiya.

Sulhu da 'yan ta'adda da 'yan taware?

A makon nan ne Gwamnatin Muhammadu Buhari tace ta bar kofar yin sulhu da Shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu da takwaransa, Sunday Igboho a bude.

Ministan shari'a na kasa watau Abubakar Malami SAN yace akwai yiwuwar Gwamnatinsu ta sasanta da wadannan mutane da yanzu duk ake shari'a da su a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel