Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa

  • Allah ya yi wa Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, jikar Sardauna ta farko rasuwa
  • Marigayiyan ta rasu ne tana da shekaru 61 a duniya kuma ta bar 'ya'ya guda uku
  • An yi mata sallar jana'iza a gidan Sardauna da ke Diori Hammani road a Sokoto

Jihar Sokoto - Jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya.

Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa
Marigayiya Hadiza Shehu Kangiwa, jikar Sardauna ta farko. Hoto: Neptune Prime
Source: Facebook

Marigayiyar diyar Wamban Kano ne, Abubakar Dan Maje.

Hajiya Hadiza ta auri tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sokoto, Shehu Kangiwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Read also

Da Duminsa: A karon farko, Shekarau ya fita rangadi da sabon shugaban APC na tsaginsu a Kano

Ta rasu ta bar 'ya'ya uku kuma an yi mata sallar jana'iza a gidan marigayi firimiyan arewa da ke Diori Hammani road a Sokoto.

Yar Tafawa Balewa ta tabbatar da rasuwar Hajiya Hadiza

Jaridar Neptune Prime ta ruwaito cewar kawarta, Hajiya Binta Tafawa Balewa, yar firimiyan farko kuma tilo na Nigeria, Alhaji Abubakar Tafawa Balewa:

"Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa matar marigayi Alhaji Shehu Kangiwa, tsohon gwamnan jihar Sokoto ne.
"Ita ce jikar Sardauna ta farko kuma 'yar babban 'yarsa, Hajiya Inno Ahmadu Bello.
"Mahaifin ta shine Wamban Kano, marigayi Abubakar Dan Maje, babban dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na I."

Wani daga cikin 'yan uwanta, Alhaji Shehu Aliyu Maradun ya ce marigayiyar ta kasance mai saukin kai duk da irin girma da daraja na gidan da ta fito.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel