Jerin sunaye: Rundunar soji ta yi wa janarori 12 ritaya

Jerin sunaye: Rundunar soji ta yi wa janarori 12 ritaya

  • Rundunar sojojin Najeriya ta yi wa wasu janarori guda 12 ritaya a ranar Juma'a, 12 ga watan Nuwamba
  • Daga cikin wadanda aka yi wa ritaya akwai manjo janar 10 sai kuma wasu Birgediya Janar guda biyu
  • An gudanar da fareti na musamman domin karrama manyan jami'an sojin a jihar Kaduna

Jihar Kaduna - A ranar Juma'a, 12 ga watan Nuwamba, rundunar sojojin Najeriya ta yi wa wasu janarori guda 12 ritaya a wani gagarumin taro da aka gudanar a jihar Kaduna.

Faretin ritayar janarorin na daga cikin shirye-shiryen da ke gudana a taron shekara na shugabancin sojojin a cibiyar rundunar da ke Jaji na jihar Kaduna.

Jerin sunaye: Rundunar soji ta yi wa janarori 12 ritaya
Jerin sunaye: Rundunar soji ta yi wa janarori 12 ritaya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an fara taron na kwanaki hudu a ranar 10 ga watan Nuwamba.

Read also

Dangote da jerin mashahuran masu kudin Afrika 5 da suke cikin Attajiran Duniya a 2021

Ga jerin sunayen janarorin da aka yi wa ritaya a kasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manjo Janar

1. Lamidi Adeosun, tsohon shugaban manufofi da tsare-tsare, hedkwatar rundunar sojoji

2. M.D. Abubakar

3. I. Birigeni

4. C.M. Abraham

5. A.C.C. Agundu

6. T.O.B. Ademola

7. A.M. Jalingo

8. A.S. Maikobi

Birgediya Janar

9. M.A. Bashirudeen

10. D.M. Onoyiveta

Jaridar ta kuma rahoto cewa akwai wasu janarori buyu da aka yi wa ritaya wadanda ba a ambaci sunayensu ba.

Da yake magana a madadin janarorin masu ritaya, manjo Janar Adeosun (mai ritaya) ya ce faretin ritayar na daga cikin al'adar rundunar sojin.

Ya kuma bukaci jami’an da ke ci gaba da aiki da kada su yi kasa a gwiwa wajen sauke hakokin da ya rataya a wuyansu, inda yace rundunar ta dade tana tattalin kimar da take da shi a idon duniya.

Read also

Dantata, Ojukwu, Da Rochas da sauran masu kudin da suka shahara kafin samun ‘yancin-kai

Cikakken sunayen janarori 114 da sauran sojin kasa da aka sauyawa wurin aiki

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa Shugaban sojin kasa na Najeriya, Faruk Yahaya, ya amince da sauyin wurin aikin hafsin soji 526 dake rundunar sojin kasa zuwa wurare daban-daban na kasar nan.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, wannan girgizar an sanar da ita ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Julin 2021.

Jaridar ta sanar da cewa an sauyawa sojojin 526 wurin aiki. Daga ciki akwai 51 masu mukamin manjo janar, 63 masu mukamin birgediya janar yayin da 39 ke da mukamin kanal.

Sauran 13 masu mukamin laftanal kanal, 166 manjo, 93 kyaftin, 92 laftanal da tara masu mukamin laftanal na biyu.

Source: Legit.ng

Online view pixel