Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa

Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa

  • Wani kwamiti da NHRC ta kafa domin bincike na musamman a kan EndSARS ya sake yin zama.
  • A karshen zaman da aka yi a ranar Talata, an bukaci a gurfanar da Abba Kyari da Vincent Makinde.
  • Ana neman Kyari ya kare kansa bayan an nemi wani mutumi da ya bace bayan IRT ta kama shi a 2018.

Abuja - Kwamitin da yake bincike na musamman a kan zargin cin zarafin mutane da ‘yan sanda suke yi, ya bukaci a kawo masa su Abba Kyari a gabansa.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Talata, tace wannan kwamitin ya bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban dakarun IRT, Abba Kyari.

Kwamitin ya bukaci a kawo masa DCP Kyari a dalilin bacewar wani da ake zargi da laifi. An kama wannan mutum ne a 2018, yanzu ba a san inda yake ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Rahoton yace kwamitin binciken yana so ya zauna da Kyari da kuma wani jami’in ‘yan sanda wanda yake matsayin sufeto a wurin aiki, Vincent Makinde.

Ana sa ran wadannan jami’ai biyu za su bayyana a gaban kwamitin mai mutum 11 a ranar 26 ga watan Nuwamba, domin jin ta bakinsu a binciken da ake yi.

Me ya kai ake neman su Abba Kyari?

Tun a shekarar 2018 ne dakarun IRT (a wancan lokaci a karkashin jagorancin Abba Kyari), suka yi ram da Mista Morris Ashwe a garin Makurdi, jihar Benuwai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Raphael Ashwe wanda ‘danuwan wannan mutumi ne ya kawo korafi gaban kwamitin, yace ba a sake ganin ‘danuwansu tun da aka wuce da shi Abuja ba.

Abba Kyari
DCP Abba Kyari a Majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamitin Suleiman Galadima ya zauna

Garba Tetengi wanda ya jagoranci zaman kwamitin na ranar 9 ga watan Nuwamba a madadin Suleiman Galadima, ya dage a kan sai an kawo 'yan sandan.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

Tetengi ya umarci babban jami’in ‘yan sanda, James Idachaba ya tabbatar cewa ya fito da Vincent Makinde da Kyari, domin su kare kansu daga wannan tuhuma.

Sai dai ba wannan ne karon farko da kwamitin da hukumar NHC mai kare hakkin al’umma a Najeriya ya bada umarni, amma jami’an tsaron suka bijire ba.

Zargin da ke kan Abba Kyari

Kwanaki ku ka ji cewa an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari na hannu a badakalar Hushpupi.

Shugaban kwamitin da Sufeto Janar na 'yan sanda na kasa ya nada domin ayi bincike, DIG Joseph Egbunike, ya gabatar da kundin sakamakon bincikensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel