Yanzu-yanzu: An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton
- Bayan makonni da kafa kwamitin bincike, an kammala binciken Abba Kyari
- Shugaba kwamitin ya mika takardun sakamakon binciken ga Sifeto Janar
- IGP Alkali ya yi alkawarin tabbatar da cewa an yi gaskiya da adalci
Abuja - Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari.
Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.
Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki da yammacin nan a shafin hukumar.
A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da mambobinta da wannan aiki na bincike mai muhimmanci.
Ya bayyana cewa:
"Kwamitin ta fara bincike ba tare da bata lokaci ba kuma wannan kundin rahoton ya kunshi diddigi da gaskiyar abinda ya faru. Hakazalika kundin ya kunshi maganganun Abba Kyari da wasu da ke da alaka da lamarin."
Bayan gabatar da rahoton, IGP Alkali ya godewa kwamitin bisa aikin da sukayi kuma yayi alkawarin cewa za'a duba rahoton kuma za'a dauki matakin da ya kamata.
Me ya faru da DCP Abba Kyari?
FBI ta yi zargin Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya bai wa Abba Kyari N8m ko $20,600, don kamawa da tsare wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Vincent.
Legit.ng ta tattaro cewa batun na cikin takardar da Kotun Amurka ta bayar na gundumar tsakiyar California mai dauke da kwanan wata 12 ga Fabrairu, 2021.
Takardar ta yi zargin cewa Hushpuppi ya ba Kyari kwangila bayan da Chibuzo ya yi barazanar fallasa wani zamba na dala miliyan 1.1 da suka aikata a kan wani dan kasuwa na kasar Qatar.
A cewar rahoton, shafi na 59, sakin layi na 145 na takardar ya bayyana cewa Kyari ya bayar da bayanan asusu na wani asusun bankin Najeriya mai dauke da sunan da ba nashi ba.
Abba Kyari ya musanta wannan zargi
DCP Abba Kyari ya jaddada cewa shi fa yana da gaskiya kan tuhumar da ake masa kuma nan ba da dadewa ba gaskiya zai bayyana.
Abba Kyari ya sake magana ne a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon tsaffin wadanda suka halarci wani taro a Amurka.
Yace dukkan abubuwan da ya fada kuma ya daura a shafinsa gaskiya ne.
Asali: Legit.ng