Da Duminsa: Matar babban malamin addini, Taiwo Odukoya, ta rigamu gidan gaskiya

Da Duminsa: Matar babban malamin addini, Taiwo Odukoya, ta rigamu gidan gaskiya

  • Babban fasto a cocin Fountain of Life Fasto Taiwo Odukoya, ya rasa matarsa ta biyu
  • Matar faston ta rasa ranta ne bayan fama da ciwan daji na tsawon shekara biyu, a cewar cocin
  • Malamin addinin kiristan ya rasa matarsa ta farko ne shekara 16 da ta gabata a hatsarin jirgi

Shekara 16 bayan matarsa ta farko ta mutu a hatsarin jirgi, Fasto Taiwo Odukoya, na cocin Fountain of Life ya sake rasa matar da ya aura bayan wancan lamarin.

A cewar sanarwan da cocin ta fiyar, Matar babban malamin addinin ta mutu ne ranar Talatan nan da muke ciki da yamma.

Dailytrust ta ruwaito cewa marigayya matasa faston ta sha fama da ciwan daji na tsawon shekaru biyu.

Fasto Taiwo
Da Duminsa: Matar babban malamin addini, Taiwo Odukoya, ta rigamu gidan gaskiya Hoto: punchng.com
Source: UGC

Abinda sanarwan ta ƙunsa

Wani sashin sanarwan da cocin ta fitar yace:

Read also

Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

"Cikin jimami da miƙa lamarin mu ga Allah, muna sanar da mutuwar matar babban Faston mu, Fasto Nomthi Odukoya."
"Ta mutu ne bayan fama da ciwan daji na tsawon shekaru biyu, ta yi iya bakin kokarinta amma kuma ta ƙarisa. Muna son ta da dukkan zuciyoyin mu, amma su waye mu da zamu yi fito na fito da kaddarar Allah.
"Gaskiyar ita ce wajibi watarana a rayuwar mu, muɓyi bankwana. Saboda haka a yanzun muna bankwana da Nomthi Odukoya, sai mun sake haɗuwa."

A wani labarin kuma Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure

Wasu miyagun yan bindiga sun yi yunkurin garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a wurin bikin aure.

Honorabul Usoro Akpanusoh, ya bayyana cewa maharan shi suka so sace wa amma ya samu nasarar tserewa, amma sun kashe mutum 2.

Source: Legit.ng

Online view pixel