'Yan bindiga sun yi garkuwa da waɗanda suka tafi kai musu kayan abinci da kuɗin fansa a daji

'Yan bindiga sun yi garkuwa da waɗanda suka tafi kai musu kayan abinci da kuɗin fansa a daji

  • Yan bindiga da suka sace masallata a jihar Niger sun sake yin garkuwa da wasu mutane biyu da suka tafi kai musu kudin fansa
  • Wasu majiyoyi daga garin Mashegu sun tabbatar da hakan inda suka ce yan bindigan sun bukaci a kai musu N200,000 da kayan abinci
  • Sai dai bayan an kai musu kayan abincin da ya kunshi shinkafa, manja, Maltina da wasu abubuwan, sun rike mutanen, suka ce abincin ya yi kadan

Jihar Niger - 'Yan fashin daji da suka yi garkuwa da masallata a baya-bayan nan a karamar hukumar Mashegu a jihar Niger sun yi garkuwa da mutane biyu da suka tafi kai musu abinci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa abubuwan da suka kai musu sun hada da katon din Maltina, gallan din manja, buhuhunan shinkafa da wasu kayayyakin abincin.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu

'Yan bindiga sun yi garkuwa da waɗanda suka tafi kai musu kayan abinci da kuɗin fansa a daji
'Yan bindiga sun yi garkuwa da waɗanda suka tafi kai musu kayan abinci da kuɗin fansa a daji a Niger. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Da farko, masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa, amma wata majiya daga garin ta shaidawa Daily Trust cewa yan bindigan sun rage kudin zuwa N200,000, sannan suka nemi a kai musu kayan abincin.

Majiyoyi sun tabbatar da afkuwar lamarin

Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar Juma'a, an kai musu N200,000, katon din Maltina, galolin manja da wasu kayan abinci, amma sun rike mutum biyu da suka kai musu kayan abincin, sun ce ya yi kadan.
"Mun kashe kusan N50,000 wurin siyan kayan abincin kawai. Sun ce muna musu wasa da hankali."

Wani majiyar daban ya tabbatar da abin da na farkon ya rahoto, yana cewa:

"Har yanzu, mutanen nan ba su sako mutanen mu ba. Sun ce mu kawo musu N200,000 da kayan abinci."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun harbe wasu daga cikin masu ibada 60 da suka sace a Kaduna, sun aiko da sako

Da ya ke martani, DSP Wasiu Abiodun, kakakin yan sandan jihar Niger ya ce rundunar tana iya kokarinta domin ceto wadanda aka sace din yana cewa yan sanda ba su goyon bayan biyan kudin fansa.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel