Da Duminsa: Yan bindiga sun harbe wasu daga cikin masu ibada 60 da suka sace a Kaduna, sun aiko da sako

Da Duminsa: Yan bindiga sun harbe wasu daga cikin masu ibada 60 da suka sace a Kaduna, sun aiko da sako

  • Barayin da suka sace masu ibada 60 a jihar Kaduna, sun bude wa mutum 5 daga cikinsu wuta ranar Asabar
  • Shugaban CAN, reshen jihar Kaduna, John Hayab, yace biyu daga ciki sun mutu, yayin da sauran ke gadon asibiti suna karban magani
  • CAN ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a faɗin kasar nan da na ƙasashen waje, su taimaka a ceto rayuwar mutanen

Kaduna - Barayin da suka sace mutane 60 suna tsaka da ibada a cocin Emmanuel Baptist dake Kakau Daji, karamar hukumar Chikun, sun harbe mutum 2 har lahira.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton yadda yan bindiga suka farmaki cocin makon da ya shuɗe, suka kashe mutum ɗaya, kuma suka sace wasu.

Dailytrust ta rahoto cewa a ranar Jumu'a, ɓarayin suka bukaci a kai musu buhunan shinkafa, jarkokin man gyaɗa, wanda a cewarsu zasu yi amfani da su wajen ciyar da mutanen.

Read also

Kotu ta zabi ranar zaman kan karar da Sheikh Zakzaky ya shigar kan Gwamnatin tarayya

Yan bindiga
Da Duminsa: Yan bindiga sun harbe wasu daga cikin masu ibada 60 da suka sace a Kaduna, sun aiko da sako Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Hakanan kuma sun gargaɗi mutanen yankin kan a gaggauta kai musu kayayyakin da suka nema ko kuma su bar mutanen da yunwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa suka kashe mutum biyu?

Shugaban ƙungiyar kiristoci reshen Kaduna, John Hayab, yace maharan sun bindige mutum biyu daga cikin waɗan da suka sace.

Hayab yace:

"Yan bindigan sun buɗe wa mutum 5 daga cikin waɗan da suka sace wuta a ranar Asabar, mutum biyu sun mutu yayin da sauran uku suka jikkata, a halin yanzun suna asibiti."
"Rayuwar masu ibadan da aka sace a Kaduna tana cikin hatsari kuma akwai bukatar gaggauta shigowar gwamnati da hukumomin tsaro."
"CAN na kira ga mutane, ƙungiyoyi, da waɗan da ke kan madafun iko musamman gwamnatin tarayya da su taimaka su ceto mutanen nan."

Sai an haɗa karfi da karfe - CAN

Shugaban CAN ya kara da cewa matsalar da suke fama da ita tafi karfin mutum daya ya magance ta, wajibi a hada karfi da ƙarfe, kamar yadda Vanguard ra rahoto.

Read also

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

Daga karfe, Hayab ya yi kira ga mabiya addinin kirista da su ƙara haɗa kansu wajen yaƙar waɗan nan azzaluman masu garkuwa.

A wani labarin kuma wata yar bautar kasa NYSC ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno

Mahaifiyar Zaynab ce ta samar mata da canjin wuri, bayan da farko an tura ta jihar Borno, inda ta ɗauki horo na tsawon mako uku.

Wani daga cikin yan uwanta yace ba su so zuwan ta jihar Borno ba,.amma da sun san haka zata faru da sun barta a can.

Source: Legit.ng

Online view pixel