Jam'iyyar APC a Gombe ta nemi Danjuma Goje ya bada hakuri bisa abinda ya faru ranar Juma'a

Jam'iyyar APC a Gombe ta nemi Danjuma Goje ya bada hakuri bisa abinda ya faru ranar Juma'a

  • Jam'iyyar APC a jihar Gombe ya yi Alla-wadai bisa abin da ya auku ranar Juma'a yayinda Sanata Danjuma Goje ke niyyar shiga jihar
  • Daukacin shugabannin jam'iyyar sun nemi tsohon Gwamnan ya nemi afuwar Gwamna Inuwa bisa abinda ya faru
  • Sabon rikici ya kunno kai cikin jam'iyyar APC a jihar Gombe yanzu haka

Gombe - Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta bukaci tsohon gwamnan kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje ya bada hakuri bisa abinda ya faru ranar Juma'a.

Shugabannin jam'iyyar a zamansu na majalisar zartarwa da sukayi ranar Asabar, sun yi Alla-wadai kan abin takaicin da ya janyo asarar rayuka a Gombe a jiya, sakamakon ziyarar da Sanatan ya kai Gombe.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na jiha, Ambasada Moses Kyari ne ya bayyana makomar jam’iyyar a gaban manema labarai a sakatariyar jam’iyyar dake Gombe.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar zaman kan karar da Sheikh Zakzaky ya shigar kan Gwamnatin tarayya

Jam'iyyar APC a Gombe
Jam'iyyar APC a Gombe ta nemi Danjuma Goje ya bada hakuri bisa abinda ya faru ranar Juma'a Hoto: Abdul No Shaking
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta bukaceshi ya bada hakuri

Yace jam'iyyar ta kuma bukaci Sanatan da ya bada hakuri ga al'ummar jihar Gombe da kuma shugabancin jam'iyyar kan irin wannan rashin zaman lafiya da ya jagoranta a jihar.

Hakazalika, jam’iyyar ta yi gargadi ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar cewa za ta amince da duk wani abu da zai kara kawo cikas ga zaman lafiya ba.

Danjuma Goje ne ya kawo yan kalare Gombe, ba hari aka kai masa ba, Gwamnatin jihar

Jihar Gombe ta caccaki tsohon gwamnanta kuma Sanata mai wakiltan mazabar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, bisa rikicin da ya auku cikin jihar.

Kwamishanan labaran jihar, Julius Ishaya Lepes, a jawabin kar ta kwana da ya saki da yammacin Juma'a ya bayyana cewa Sanata Goje da kansa ya haddasa wannan rikicin.

Kara karanta wannan

Danjuma Goje ne ya kawo yan kalare Gombe, ba hari aka kai masa ba, Gwamnatin jihar

Yace dama halin tsohon gwamnan ne tattara yan kalare duk lokacin duk zai shigo jihar.

Gwamnatin ta kara da cewa har yanzu Goje ya lashe takobin tura yan kalare hana jama'a sakat da zaman lafiya.

Tace ba zata zuba ido wasu yan siyasa su tayar da rikici cikin jihar da zai haddasa asarar rayuka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel