An yiwa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Orji Kalu nadin sarauta a kasar Argungun

An yiwa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Orji Kalu nadin sarauta a kasar Argungun

  • Sarkin Argungun ya yiwa Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sarautar Ganuwan Kabi ranar Juma'a
  • Hakazalika a taron nadin, an yiwa tsohon gwamnan Abia kuma Sanata Orji Uzor Kalu sarautar Kibiyan Kabi
  • Gwamnonin, Sarakunan gargajiya da kuma yan majalisar dokokin tarayya ne suka halarci wannan taro

Kebbi - Mai martaba Sarkin Argungun, Alhaji Samaila Muhammadu Mera, a ranar Juma'a a jihar Kebbi, ya nada Shugaban Majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin Ganuwan Kabi.

Wannan nadi na cikin bukukuwan cikar Sarkin Argungun shekaru 25 kan karagar mulki, Ola Awoniyi mai magana da yawun Ahmad Lawan ya sanar.

Wadanda aka yiwa nadu kuma a bikin sune tsohon Gwamnan jihar Abia kuma mai tsawatarwa a majalisa, Orji Uzor Kalu(a matsayin Kibiyan Kabi), da kuma Shugaban kamfanin wutan lantarkin Kaduna KEDC, Engr Garba Haruna Argungu.

Read also

Gwamna El-Rufai ya dauko Farfesa daga Ingila, ya nada shi a matsayin Mai bada shawara

Wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnonin, Sarakunan gargajiya da kuma yan majalisar dokokin tarayya.

Daga cikin gwamnoni akwai jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni; da Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An nada shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, matsayin Ganuwan Kabi
An nada shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, matsayin Ganuwan Kabi Hoto: Tope Brown
Source: Facebook

Sarakunanan Gargajiyan da suka halarta

Daga cikin Sarakunan gargajiya kuwa akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III; Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; da Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb Bamalli.

Sauran sune Sarkin Bade, Sarkin Biu, Sarkin Machina, Sarkin Lafiya, Sarkin Zuru da Sarkin Zamfara.

Cikin yan majalisa kuwa akwai Sanata Barau Jibrin, Sanata Muhammad Musa Bello, Sanata Chukwuka Utazi, Yahaya Abdullahai, Sen. Shuiabu Iau, Sen. Michael Nnanji.

An nada shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, matsayin Ganuwan Kabi
An nada shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, matsayin Ganuwan Kabi Hoto: Tope Brown
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel