Bawan Allah ya siya jirgin sama, ya mayar da shi gida da bandaki, bidiyon ya bada mamaki

Bawan Allah ya siya jirgin sama, ya mayar da shi gida da bandaki, bidiyon ya bada mamaki

  • Wani mutum mai suna Bruce Campbell a kasar Amurka ya siya tsohon jirgin sama wanda ya mayar da shi gida mai kyau
  • Bruce wanda ya siya tsohon jirgin a kan $100,000 (N41 million) a shekarar 1999 ya koma zama cikin jirgin na tsawo wata shida a shekara
  • Injiniyan mai ritaya ya kashe $120,000 (N49 million) inda ya kwance jirgin kuma ya mayar da shi gida mai matukar kyau a Portland

Ba kamar jama'a da je zama a gidaje ginannu ba, wani mutum ya yanke shawarar zama cikin jirgin sama.

Dan asalin kasar Amurkan mai suna Bruce Campbell ya siya jirgin da aka kera tun a shekarar 1969 a 1999 a kan farashi $100, 000 (N41 million).

Bawan Allah ya siya jirgin sama, ya mayar da shi gida da bandaki, bidiyon ya bada mamaki
Bawan Allah ya siya jirgin sama, ya mayar da shi gida da bandaki, bidiyon ya bada mamaki. Hoto daga UNILAD Tech
Asali: Facebook

A kokarin Bruce na mayar da jirgin saman yadda ya ke so, ya sake kashe wasu kudi har $120, 000 (N49 million) domin gyara shi bayan ya mayar da shi wani filin shi da ke Portland.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Ya cire dukkan kujerun cikin jirgin

Tsohon injiniyan ya sake gyara jirgin inda ya cire dukkan wuraren zama tare da karawa da wurin wanka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da gyara wurin da dukkan abubuwan da ake bukata a cikin gida kamar yadda UNILAD Tech ta wallafa bidiyon. A halin yanzu, ya na kwashe wata 6 a cikin jirgin a kowacce shekara.

A daidai inda wurin tukin jirgin ya ke, a nan ya ke zama ya dinga karance-karancensa.

Bruce ya ce ya dace a dinga mayar da tsoffin jiragen sama zuwa gidaje

Tsohon ya ce ya dace a dinga mayar da tsoffin jiragen sama zuwa gidaje domin guje wa asara.

A kalamansa:

"Watsar da kyakyawan jirgin sama ya zama bola babbar asarar ce kuma bai dace a dinga yin ta ba."

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka

Andrew Breckon ya yi tsokaci da:

"Gaskiya wannan babbar dabara ce, amma zai lashe dubu dari biyu da ashirin kuma kada a yi batun cewa akwai filin da za a dora tsohon jirgin. Gaskiya bai kai kyan da ake magana ba kuma dai cikin shi ya hadu."

Kathleen Ketchell ya ce:

"Gaskiya ya yi dabara amma da a ce ni ne, zan cire wadannan bishiyoyin da ke kusa da jirgin don gudun gobara a lokutan sanyi."

Sylvana Rodriguez cewa tayi:

"A gaskiya wannan ba dabara mai kyau ba ce. Ta dogara ne da inda ka ajiye jirgin saman. A Arizona, zai kasance har abada amma idan aka saka shi a yankuna masu zafi, sai godiya.
"Kwata-kwata mutum ba zai ji dadinsa ba. Na ga motoci da aka mayar da su wuri fiye da haka. Ba su yi kama da gidaje. Wannan mutumin bashi da aure, mace ba za ta zauna a nan ba."

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel