Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

  • Matasa dauke da makamai da ake kyautata zaton yan daba ne sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe
  • A safiyar yau Juma'a 5 ga watan Nuwamba ne Sanata Goje da tawagarsa suka dira filin jirgin Gombe da nufin shiga gari ɗaurin aure
  • Sai dai a hanyarsu ta zuwa garin sun tarar da matasan dauke da makamai suna ƙone-ƙone a kan babban titin Gombe-Bauchi

Jihar Gombe - Wasu da ake zargin yan daba ne, a ranar Juma'a, sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe.

Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan daba hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Read also

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe-Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa an fasa gilashin wasu motocci, wasu kuma aka ƙona su.

Ya kara da cewa mutane da dama sun yi rauni sakamakon lamarin.

Dubban matafiya sun yi cirko-cirko a hanyoyin biyu, duba da cewa babu motar da aka bari ta wuce.

An tura jami'an tsaro su kwantar da tarzomar duba da cewa akwai matasa a ɓangarorin biyu ɗauke da makamai.

Daily Trust ta ruwaito cewa ba a ga maciji tsakanin Goje da tsohon yaronsa, Gwamna Muhammadu Inuwa, a baya-bayan nan kan iko da jam'iyyar APC a jihar.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Gombe, SP Obed Mary Malum amma hakan bai yi wu ba domin bata ɗaga waya ba.

Read also

Karin bayani: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel