Da dumi: An samu kwayar maganin cutar Korona, za'a fara amfani shi a kasar Birtaniya

Da dumi: An samu kwayar maganin cutar Korona, za'a fara amfani shi a kasar Birtaniya

  • Bayan tsawon watanni ana gudanar da bincike da gwagwarmaya, kamfanin Merck, ya kirkiri kwayar maganin Korona
  • Kamfanin ya ce gwajin da aka yi a watan Oktoba ya nuna cewa an rage adadin masu bukatar zuwa asibiti jinyan Korona
  • Wasu masana sun bayyana cewa ana tsoron kada maganin ya rika haifar da matsaloli wajen haihuwa

London - A ranar Alhamis, Kasar Birtaniya ta zama kasa ta farko a duniya da ta amince da fara baiwa masu cutar Korona sabon maganin da aka kirkira, hukumar lura da magunguna ta kasar MHRA ta sanar.

Ministan kiwon lafiya Birtaniya, Sajid Javid, ya bayyana cewa daga yanzu mutane zasu iya jinyar kansu daga gidajensu, SkyNews ta ruwaito.

A jawabinsa yace:

"Yau ranar tarihi ne ga kasarmu, saboda UK ce kasa ta farko a duniya da zata amince da amfani da maganin cutar COVID-19,"

Kara karanta wannan

Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi

Muna kokari tare da NHS domin tsara shirin rabawa marasa lafiya maganin molnuopiravir."

A riwayar CBS News, masu shekaru akalla 18 ne zasu iya amfani da kwayar maganin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana cewa maganin mai suna molnupiravir, za'a rika sha ne sau biyu a rana na tsawon kwanaki biyar.

An samu kwayar maganin cutar Korona
Da dumi: An samu kwayar maganin cutar Korona, za'a fara amfani shi a kasar Birtaniya Hoto: Merck's Pill
Asali: Facebook

Wasu kasashen fa?

A Amurka kuwa, hukumomi na tattaunawa har yanzu kan kwayar maganin Molnupiravir.

Hakazalika gammayar kasashen Turai.

A watan Oktoba, hukumar lura da ingancin abinci da magani na kasar Amurka ta sanar da cewa zata kira taron masana masu zaman kansu domin duba kyawun wannan magani da kuma ingancinsa.

Zasu tattauna ne a kasar Nuwamba.

Menene ra'ayin masana kan wannan?

Kamfanin da ya kirkiri maganin, Merck, ya bayyana cewa gwajin da aka yi a watan Oktoba ya nuna cewa an rage adadin masu bukatar zuwa asibiti jinyan Korona da rabi da wannan magani.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas

Har yanzu babu wata mujjalar masana kimiyya da ta duba wannan magani kuma ta wallafa bincike kansa.

Wasu masana sun bayyana cewa ana tsoron kada maganin ya rika haifar da matsaloli wajen haihuwa ko kuma cututtuka yayin haihuwa.

Sun bayyana hakan kan yadda maganin ke datse tafiyar kwayoyin cututtuka.

Gwamnatin tarayya za ta hana ma'aikata zuwa aiki idan ba suyi rigakafin Korona ba

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga Disamba, 2021, duk ma'aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona ba ba zai samu damar shiga ofis ba.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel