Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi

Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi

  • An gurfanar da wani Mu'azu Magaji Danbala a gaban kotu da ke zamanta a Nomansland a Kano kan cin mutuncin Gwamna Abdullahi Ganduje
  • An yi karar Danbala ne da wani mutum kan hadin baki da wallafa hoton Gwamna Ganduje da yayansa biyu a Facebook tare da kiransu 'Barayin Kano'
  • Wanda ake zargin ya musanta tuhumar da ake masa ya kuma nemi a bada shi beli amma lauyan mai shigar da kara bai amince ba don haka aka tsare shi

Jihar Kano - Wata kotu da ke zamanta a Nomansland ta bada umurnin a tsare wani Mu'azu Magaji Danbala saboda taɓa mutuncin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ana tuhumar wanda ake zargin ne da furta kalaman cin mutunci ga gwamnan da yaransa biyu; Abdulaziz da Balaraba a Facebook.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi
An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ɗayan wanda ake zargin mai suna Jamilu Shehu har yanzu bai shigo hannu ba.

An gurfanar da mutanen biyu ne kan hadin baki, zagi da gangan, tada zaune tsaye da ɓata suna wanda hakan sun saba da sashi na 97, 114, 391 da 399 na Penal Code.

A cewar bayanin farko, a ranar 26 ga watan Oktoban 2021, Ciyaman din ƙaramar hukumar Nasarawa, Auwal Lawal Shuaibu ya shigar da korafi wurin hukumar binciken sirri na musamman, SIB, kan mutanen biyun mazauna Ƙiru a Kano.

Rahoton na farko ya ce:

"A ranar da aka ambata da farko, ku biyu kun haɗa baki kun wallafa hotunan mai girma Gwamnan Kano, har da yaransa biyu ɗauke da rubutu mai cewa 'Ɓarayin Kano' tare da sanin cewa abin da kuka aikata zai iya tada rikici a Kano da wajen Kano.

Kara karanta wannan

Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru

"Don haka ana zargin ku da aikata laifukan da aka ambata tunda farko."

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa kuma suka nemi beli.

Daga nan kotu ta bada umurnin a tsare mata wanda ake zargin bayan ƙin amincewa da bukatarsa ta neman beli.

An dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban 2021.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel