Gwamnatin tarayya za ta hana ma'aikata zuwa aiki idan ba suyi rigakafin Korona ba
- Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hana wadanda suka ki yin rigakafin Korona zuwa aiki
- Duk wanda kuma ba zai yi ba ya shirya yin gwajin Korona bayan sau biyu mako-mako
- Wannan abu zai shafi ma'aikatan gwamnatin tarayya ne kadai
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga Disamba, 2021, duk ma'aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona ba ba zai samu damar shiga ofis ba.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, rahoton DailyTrust.
Mustapha wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar Korona ya ce kowani ma'aikaci daga lokacin zai rika bayyana takardar hujjar yin rigakafi ko sakamakon gwajin Korona da ya nuna bai da cutar kafin ya samu shiga ofis.
A cewarsa:
"Fari daga ranar 1 ga Disamba, 2021, za'a bukaci ma'aikatan gwamnatin tarayya su bayyana hujjar cewa sun yi rigakafi ko sakamakon gwajin Korona da aka yi cikin kwanaki uku, kafin a bari su shiga ofishohinsu."
"Za'a wallafa sanarwa na musamman kan wannan lamari."
A cewarsa, lissafi ya nuna cewa cikin makonni hudu da suka gabata, an samu saukin adadin masu kamuwa da cutar a wasu jihohi yayinda abun ke yawaita a wasu jihohi.
Ya ce tun da cutar ta bulla a Najeriya kawo yanzu, an yiwa mutane 3,141,795 gwaji.
Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba
Gwamnatin jihar Edo, karkashin jagorancin gwamna Obaseki ta fara aiwatar da dokar "Ba rigafin korona, babu aiki" a ma'aikatun jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamna Obaseki na jihar Edo, shine gwamna na farko a Najeriya da ya hana mutanen da ba'a musu rigakafin cutar COVID19 ba shiga wuraren gwamnati.
Duk da cewa da farko an yi watsi da kudirin gwamnan, amma Obaseki bai yi kasa a guiwa ba wajen aiwatar da kudirinsa.
A ranar Laraba da safe, jami'an lafiya da kuma jami'an tsaro sun kafa madakata a kofar shiga ma'aikatun Benin, Babban birnin jihar, inda suke tabbatar da an bi umarnin gwamna.
Asali: Legit.ng