‘Yan Boko Haram sun sace matafiya, sun dawo da Musulmai, sun yi gaba da sauran fasinjoji

‘Yan Boko Haram sun sace matafiya, sun dawo da Musulmai, sun yi gaba da sauran fasinjoji

  • Sojojin kungiyar Islamic State's West Africa Province sun kai hari a kan hanyar Maiduguri-Tamsu Kawu.
  • ‘Yan ta’addan sun tare motoci takwas da ke zuwa garin Tamsu Kawu, amma daga baya sun kyale wasunsu.
  • Wadannan ‘yan ta’adda sun bukaci fasinjojin da aka kama su karanta Kur’ani, aka kyale musulman su tafi.

Borno - Wasu sojojin Boko Haram da ake zargi ‘yan bangaren ISWAP ne, sun yi ta’adi a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021 a yankin jihar Borno.

Rahotanni daga Vanguard sun ce ‘yan ta’addan sun tare motoci a hanyar Maiduguri-Tamsu Kawu-Ngamdu-Damaturu, sun dauke matafiya da-dama.

‘Yan ta’addan sun tare motocin haya da na gida akalla takwas, inda suka yi gaba da mutanen ciki.

Rahoton ya bayyana cewa wannan lamari ya auku ne da kimanin karfe 3:00 na yammacin jiya ranar Talata tsakanin gadar Tamsu Kawu da garin Ndamdu.

Kara karanta wannan

Mary Odili: Dattawan Neja-Delta sun bukaci Shugaban kasa ya yi maza, ya fito ya bada hakuri

Mafi yawan wadanda suka fada hannun ‘yan ta’addan musulmai ne. An kai fasinjojin zuwa wani rafi, inda aka bukaci duk su karanta ayoyi cikin Al-Kurani.

An sake fasinjoji, an kyale wasu 3

Bayan an yi dace mafi yawan fasinjojin sun yi karatun littafin mai tsarki, sai aka kyale su su tafi, amma aka tsare wasu mutane uku da ake zargin kiristoci ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani tsohon jami’in ma’aikatar gona na jihar Borno, wanda yana cikin wadanda aka tare ya zanta da Vanguard, kuma ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.

‘Yan Boko Haram
Wata motar mayakan ISWAP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yadda na sha da kyar ...

“A lokacin da suka yi mani tambayoyi ne, sai suka gane cewa ina fama da ciwon sukari, sannan kuma ga tsufa, wannan ya cece ni.” – Tsohon jami’in.
“Jagoran ‘yan ta’addan yace su kyale ni in shiga sahun wadanda aka kyale da karfe 7:00.”

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Wannan Bawan Allah yace ‘yan ta’addan sun zarge su da hannu a kisan Abubakar Shekau, a karshe yace dole ya godewa Ubangiji Allah da ya cece shi a ranar.

Tamsu Kawu, jihar Borno

Garin Tamsu Kawu tafiyar kilomita 80 ne zuwa babban birnin jihar Borno, Maiduguri. Kauyen yana yankin Arewa maso yamma ne da garin na Maiduguri.

Tsohon gwamna Kashim Shettima ya kashe makudan kudi wajen sake tada garin Tamsu Kawu kafin 2019, bayan ta’addancin da ‘yan Boko Haram suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel