Mary Odili: Dattawan Neja-Delta sun bukaci Shugaban kasa ya yi maza, ya fito ya bada hakuri

Mary Odili: Dattawan Neja-Delta sun bukaci Shugaban kasa ya yi maza, ya fito ya bada hakuri

  • South-South Elders Forum ba ta ji dadin abin da jami’an tsaro suka yi a gidan Alkali Mary Odili ba.
  • Kungiyar tace a shekarar 2019, an taba yi wa Mai shari’a Walter Onneghen irin wannan wulakanci.
  • Dattawan na Neja-Delta suna ganin cewa Alkalan da suka fito daga Kudu maso kudu kadai ake hari.

Delta - Wata kungiyar dattawan kudu maso kudancin Najeriya, ta yi kira ga shugaban Muhammadu Buhari ya nemi afuwar dangin Mary Odili.

A ranar Litinin, Vanguard ta rahoto kungiyar South-South Elders Forum tana cewa akwai bukatar shugaban Najeriya ya roki dangin Mary Odili su yafe masa.

Kungiyar ta Neja-Delta tana so Muhammadu Buhari ya bada hakuri ne a kan yadda jami’an tsaro suka kutsa gidan Alkalin kotun koli watau Mai shari’a Odili.

Kara karanta wannan

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

Jaridar ta kuma rahoto kungiyar tana cewa wannan ne karo na biyu da aka tura jami’an tsaro cikin gidan babban Alkali da ya fito daga yankin Neja-Delta.

A cewar kungiyar dattawan, jami’an tsaro sun yi wannan aiki ne domin a tsorata bangaren shari’a. An taba yi wa Walter Onneghen irin wannan dura.

Buhari
Buhari a fadar shugaban kasa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Wannan ya sa dattawan suke ganin cewa harin da aka kai wa Mary Odili, cin fuska ne ga mutanen kudu maso kudancin kasar nan, inda Alkalin ta fito.

Shugaban South-South Elders Forum na kasa, Anabs Sara-Igbe, ya fitar da jawabi, yana cewa ana kokarin nunawa mutanen kudu cewa Najeriya ba ta su ba ce.

Anabs Sara-Igbe ya fitar da jawabi

Mai martaba Anabs Sara-Igbe ya yi jawabi a madadin iyalin Peter Odili da mutanen Neja-Delta.

Kara karanta wannan

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

“A madadin manya da mutanen Neja-Delta, muna Allah-wadai da shiga gidan iyalin Mai girma (Dr.) Peter Odili da Alkalin kotun koli, Mary Odili.”
“Najeriya tana aiki ne da tsarin damukaradiyya wanda ya ba kowa ikonsa, saboda haka babu wani bangare da zai iya ba daya tsoro.” - Sara-Igbe.
“Saboda haka shugaban kasa ya fito ya bada hakuri ga Peter Odili da matarsa, Mary Oidli, a matsayinsa na shugaban bangaren zartarwa na Najeriya.”

Kotu tace a ba Delta fam $1.63bn

Dazu aka ji Gwamnatin Tarayya ta sha kashi a shari’arta da jihar Delta a kan wasu Dala biliyan 50 da Najeriya ta samu daga fetur, wanda jihar tace da kason ta.

Jihar Delta tace dole a ba ta 13% daga cikin wadanan makudan kudi da aka samu. Wannan ya jawo maganar ta je har gaban babban kotun tarayya na Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel