Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki

Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki

  • An gayyato Sheikh Mufti Ismail Menk ya gabatar da lakca bisa munasabar cika Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki
  • Mufti Menk yayi jawabi kan muhimmancin zaman lafiya da kuma yadda yan arewa suka dau addini da muhimmanci
  • Sarkin Musulmi ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa ganin wannan rana

Sokoto - Shahrarren Malamin addinin Musulunci a duniya, Mufti Isma'il Menk, ya gabatar da muhadara a taron cikar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Shekara 15 akan Karagar Mulki.

A jawabin da Masarautar ta saki a shafinta, Mufti Menk ya yi jawabi ne kan muhimmancin zaman lafiya.

Wannan taro ya gudana ne a dakin taron Conference Hall dake Kasarawa Sokoto.

Mufti Menk a wa'azinsa ya bayyana muhimmancin zaman lafiya ga al'umma.

Yace:

"Ba zaka taba cin nasara ba idan kana yaki da mutane kullum."

Kara karanta wannan

Jerin sunayen mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin jami’ar Abuja

Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki
Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Menk ya jinjinawa Arewacin Najeriya

Menk a jawabinsa ya bayyana abindd ya gani na yadda mutan Arewa suka dauki addini da muhimmanci musamman Sallah.

Menk yace a Arewa kadai ya ga ana cika Masallaci lokacin Sallan Asuba.

Yace:

"Wuraren da na ga an cika Masallaci lokacin Sallar Asuba shine a wannan yanki na kasar nan (Arewa)."

Sarkin Musulmi Ya karrama wasu mutane

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Karrama wasu Mutane Biyar Kan Gudumuwar da Suke Bawa Masarautar da al'ummar Musulmi.

Daga cikin wadannan mutane akwai Maryam Lemu da Yayanta Nura Lemu; 'ya'yan Margayiya Aisha Lemu Da Shiekh Ahmad Lemu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel