Duk maganar da na fada kan lamarin tsaron Najeriya ce gaskiya, ku daina sauraron yan jarida

Duk maganar da na fada kan lamarin tsaron Najeriya ce gaskiya, ku daina sauraron yan jarida

  • Ministan Labarai ya bayyanawa yan Najeriya maganar da ya fada kan lamarin tsaro ya kamata a rika saurara
  • Ya caccaki gidajen jaridan dake wallafa rahotanni da ka iya ragewa jami'an Sojojin Najeriya karfin gwiwa
  • A cewarsa, Amurka da Birtanniya kawai so suke su riga sayarwa Najeriya makamai ba taimaka mata ba

Abuja - Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa yan Najeriya su rika sauraron jawabansa saboda shi kadai ke fadin gaskiya kan lamarin tsaron Najeriya.

Lai Mohammed ya yi wannan magana ne matsayin martani ga gidajen jaridan CNN dake Amurka da kuma The Economist dake Birtaniya.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ofishinsa, rahoton SR.

Yace gidajen Jaridun kasar wajen biyu karya suke a rahotannin da suke wallafawa kan Najeriya.

Read also

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

Lai Mohammed yace abinda The Economist ta wallafa na bayani kan lamarin tsaro yake a Najeriya iri daya ne a abinda gwamnatin Amurka ta wallafa a shekarar 2020 kuma duka babu gaskiya ciki.

A cewarsa, kawai so suke su rusa Najeriya.

Yace:

"Lokacin da CNN ta wallafa rahoton karya kuma caccakesu. Ta wnai dalili zamu hada kai da wasu wajen rusa gidanmu?"
"Ta wani dalili kuke son mu hada hannu da wasu mutanen da kawai so suke son sayar mana da makamai ta hanyar zagin Sojojinmu.

Lai Mohammed
Duk maganar da na fada kan lamarin tsaron Najeriya ce gaskiya, ku daina sauraron yan jarida Hoto: Lai Mohammed

Wani rahoton Mujallar The Economist ta buga?

The Ecomist ta ruwaito cewa Hukumar Sojojin Najeriya "cike take da Janar-janar da suka gaza magance matsalar tsaron kasar."

"Hukumar Sojin Najeriya fa kawai babba ce a takarda. Amma yawancin Sojojinta gawawwaki ne kawai albashi suke karba kuma yawancin makaman hukumar sacesu akeyi ana sayarwa yan bindiga."

Read also

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

The Economist a rahoton ta bayyana cewa ta gaza magance matsalar saboda manyan hafsoshin wawure kudaden kawai sukeyi.

Source: Legit.ng

Online view pixel