Kano: 'Yan KAROTA sun yi ƙarar shugaban su, Baffa Ɗan’agundi, wurin ICPC

Kano: 'Yan KAROTA sun yi ƙarar shugaban su, Baffa Ɗan’agundi, wurin ICPC

  • Jami’an hukumar kula da titinan jihar Kano, KAROTA, sun gabatar da manajan darektan su, Baffah Baba Dan’agundi, gaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kan ta, ICPC
  • Su na zargin Dan’agundi da raba rasit na bogi ga duk ofisoshin hukumar tun shekarar 2019 da ya hau kan kujerar sa ta manajan darekta
  • Sai dai da aka nemi jin ta bakin kwamishinan ICPC na jihar Kano, Ibrahim Garba Kagara, a kan lamarin, ya ce tabbas an kai korafin shugaban KAROTA amma be fadada bayani ba

Kano - Hukumar yaki da rashawa mai zaman kan ta, ICPC ta fara bincike a kan zargin da ake yi wa Baffah Baba Dan’agundi, Shugaban hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa na jihar Kano, KAROTA.

Read also

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

Hakan ya biyo bayan wata takardar korafi ne da wasu ma'aikatan hukumar suka rubuta na zargin shugaban na KAROTA da aikata wasu abubuwa da suka saba wa doka, rahoton Daily Trust.

Kano: 'Yan KAROTA sun yi ƙarar shugaban su, Baffa Ɗan’agundi, wurin ICPC
Kano: 'Yan KAROTA sun yi ƙarar shugaban su, Baffa Ɗan’agundi, wurin hukumar ICPC. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Takardar ta zo da taken: 'Takardar korafi akan manajan darekta na hukumar kula da titinan jihar Kano (KAROTA) akan ayyukan rashawa'.

Ma’aikatan sun zargi shugaban su da fara bayar da rasit din bogi ga duk ofisoshin hukumarsu da ke jihar tun da ya dare kujerar sa a 2019.

Sun ce ya na bayar da rasit din bogin ne a hedkwatar hukumar amma ba a gabatar da shi gaban kotun hukumar ba, inda ma’aikatan amsar harajin jihar Kano, KIRS su ke amsar haraji.

Sun shaida cewa ya na hakan ne da taimakon dan’uwan sa

Read also

EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta

Kamar yadda takardar ta zo, shugaban KAROTA ya na aiwatar da wannan aika-aika ne ta hannun wani mutum mai suna Shehu, wanda dan uwansa ne ba ma’aikacin jihar Kano ba.

Yayin da a ka tuntubi kwamishinan ICPC na jihar Kano, Ibrahim Garba Kagara, ya tabbatar da cewa an kai karar shugaban KAROTA a gabansu.

Sai dai be kara fadada bayani akan takardar ba, kuma be yi wata magana mai tsawo dangane da binciken da su ke yi akan lamarin ba.

An yi kokarin jin ta bakin manajan darektan amma abin ya ci tura har lokacin rubuta rahoton nan.

Wakilin Daily Trust ya tura ma sa sako, amma be bayar da amsa ba har lokacin hada rahoton.

Kano: Hotunan ɓata gari 59 da aka kama kan zargin fashi, safarar miyagun ƙwayoyi da makaman da aka ƙwato

A baya, kun ji cewa, Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Kano ta ce ta kama mutum 59 da ake zargin masu laifi ne kuma ta kwato makamai da muggan kwayoyi a hannunsu, rahoton Daily Trust.

Read also

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Jaridar Daily Trust ta rahoto mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rahoto mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Source: Legit.ng

Online view pixel