Hukumar NAFDAC zata fara kamen masu sana'ar tallan kwayoyi a kan hanya a jihar Kaduna

Hukumar NAFDAC zata fara kamen masu sana'ar tallan kwayoyi a kan hanya a jihar Kaduna

  • Hukumar NAFDAC zata fara magance masu sana'ar siyar da kwayoyin magunguna akan hanya a jihar Kaduna
  • NAFDAC tace irin waɗannan mutanen suna wasa da rayuwar al'umma, domin sun saɓa dokokin siyar da magani
  • A cewar hukumar ya kamata mutane su gujewa siyan magani a kan hanya domin kula da rayuwarsu

Kaduna - Hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi ta kasa, NAFDAC, tace ta kammala shirye-shiryen kawo ƙarshen tallan kwayoyin magunguna a kan a jihar Kaduna.

Shugaban NAFDAC reshen Kaduna, Nasiru Mato, shine ya bayyana haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa NAN ranar Laraba a Kaduna.

Daily Nigerian ta rahoto Mato yace tallan magunguna a kan hanya kwararo-kwararo babban damuwa ne ga NAFDAC da kuma jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Ba a yi nisa ba, INEC ta fara kuka da yadda jam'iyyun siyasa ke kare jini biri jini

Masu talla a kan hanya
Hukumar NAFDAC zata fara kame masu tallan kwayoyi a kan hanya a jihar Kaduna Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa dokar hana tallan kwayoyin tana nan tana aiki kuma ya zama wajibi a kula da kowace kwayar magani kamar yadda masu haɗa magungunan suka bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene illar tallan magani akan hanya?

Mista Mato yace:

"Magunguna na shan zafi mai tsanani a hannun masu talla a kan hanya, dumamar yana yi da sauran illoli, ba zamu bar haka ya cigaba ba."
"Tallan magani ba bisa ƙa'ida ba ya saɓa wa dokoki da ƙa'idojin siyar da magunguna. Ta ya mutum zai yi sana'ar irin waɗan nan kayayyakin bayan ba shi da ilimi a kansu?"
"Masu irin wannan aikin sun saba wa dokar magunguna, dan haka ya kamata mutane su kula, su tabbatar inda zasu siya magani yana da rijista."

Wane mataki NAFDAC take ɗauka?

Shugaban ya ƙara da cewa hukumar NAFDAC na kokarin wayar dakan mutane kan gujewa masu tallan magani a kan hanya domin tsira daga hatsarinsu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

Guardian ta rahoto shi ya cigaba da cewa:

"Illar da siyan magunguna akan hanya yake da shi yana da hatsari sosai. Wajibi a dakatar da masu tallan magani na kan hanya domin suna wasa da rayuwar al'umma."

A wani labarin kuma daga jihar ta Kaduna Akalla mutum hudu sun mutu, wasu uku sun jikkata a wani rikici tsakanin makiyaya da mutanen gari

Rahoto ya bayyana cewa lamarin ya auku ne kan hanyoyin da makiyaya ke wucewa da shanunsu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai, ya nuna alhinisa tare da kira ga jama'a su daina ɗaukar doka a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel