Yanzu-yanzu: Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'YarAdu'a ya rasu a Landan

Yanzu-yanzu: Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'YarAdu'a ya rasu a Landan

  • Allah ya yi wa tsohon ministan noma da ma’adanan ruwa, Dr Abba Sayyadi Ruma rasuwa
  • Ya rasu ne a London inda ya je domin a duba lafiyar sa sakamakon ciwon suga da ya addabe shi
  • Ya rasu ya na da shekaru 59 a duniya, ya kuma bar matan aure biyu da 'ya'ya 9 duk masu rai

Tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Dr Abba Sayyadi ruma ya riga mu gidan gaskiya.

Leadership ta rahoto cewa Ruma ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan.

Kawunsa kuma Danwairen Katsina, Alhaji Sada Salisu ya tabbatar da rasuwarsa tsohon ministan

Yanzu-yanzu: Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'Yar Adu'a ya rasu a Landan
Abba Ruma, tsohon ministan Noma da albarkatun ruwa ya rasu a Landan. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar Sada, marigayin ya yi fama da ciwon sukari na tsawon lokaci kafin rasuwarsa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Allah ya yiwa mai masallacin matafiya da ke hanyar Kaduna-Zariya rasuwa

Ya rasu ya na da shekaru 59 sannan ya bar mata 2 da yara 9.

Takaitacen Tarihin Ruma

An haife shi a ranar 13 ga watan Maris na 1962, marigayi Ruma minista ne wanda ya yi aiki tukuru a lokacin mulkin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.

Ruma ya rike kujerar shugaban hedkwatar kungiyar tattalin kudi don habaka harkar noma a Rome, kasar Italiya.

Tsohon ministan ya yi digirin sa na farko a bangaren tarihi a jami’ar Sokoto, ya yi digirin sa na biyu a harkokin kasashen waje daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria sannan ya yi digirin digirgir a jami’ar Abuja.

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa

A wani rahoton, kun ji cewa jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya.

Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Hisbah sun kama Aliyu Na Idris da ke son sayar da kansa kan N20m domin talauci

An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel