Bitcoin ya sake faɗi ƙasa warwas, an rasa biliyoyin kuɗin intanet cikin 'yan mintuna

Bitcoin ya sake faɗi ƙasa warwas, an rasa biliyoyin kuɗin intanet cikin 'yan mintuna

  • Darajar kudin intanet na Bitcoin ya ruguzo kasa a kasuwannin hada-hadar kudin na duniya
  • Hakan na zuwa ne bayan darajar Bitcoin ya karu sosai a baya-bayan nan ya kai $67,000
  • Faduwar darajar ta Bitcoin ya shafi sauran kudaden intanet kamar Ethereum, Binance Coin ds

Darajar kudin intanat na Bitcoin ya sake faduwa kasa warwas, hakan yasa aka yi asarar miliyoyin fam na kudin na intanet a kasuwannin duniya, hakan ya jefa masu kasuwanci cikin fargaba.

Kudin intanet din da ya fi fice a duniya ya rage daraja ya kai kasa da $59,000 biyo bayan saukan farashinsa cikin gaggawa a kankanin lokaci da ake kira 'flash crash', Daily Trust ta ruwaito.

Bitcoin ya sake faɗi ƙasa warwas, biliyoyin kuɗin intanet sun ɓace cikin 'yan mintuna
Bitcoin ya sake faɗi ƙasa warwas, an rasa biliyoyin kuɗin intanet cikin 'yan mintuna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan babban faduwa ne na fiye da $5,000 daga matakin da ake siyansa cikin 'yan kwanaki da suka shude.

Read also

Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN

Hakan na zuwa ne kimanin mako daya bayan darajar Bitcoin ta daga sosai zuwa $67,000.

Yadda faduwar darajan Bitcoin ya shafi sauran kudaden intanet

Faduwar darajar Bitcoin zai shafi sauran kudaden intanet da suka hada da thereum, Binance Coin, Cardano, Solana da Ripple wanda a yanzu suma darajarsu ta yi kasa.

Farashin Etherium ya ragu da kashi 6 cikin 100 zuwa $4 a cikin awa 24 da ya wuce, a cewar alkalluman baya-bayan nan daga CoinDesk.

Darajar Cardano shima ya yo kasa da kusan kashi 9 cikin 100 a cikin kwana guda zuwa kasa da $2, yayin da Solana ya fadi da kashi 8.05 zuwa $190.

Faduwar farashin na ranar Laraba ya faru sakamakon siyar da Bitcoin a farashi mai tsada da masu tsohuwar ajiya suka yi don samun riba.

Read also

Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu

Wannan abu ne da ya saba faruwa a duk lokacin da farashin kudin crypto ya yi daraja sosai.

Akwai yiwuwar wannan faduwar farashin zai janyo hankalin sabbin masu siyan Bitcoin.

A cewar masu nazarin harkar, an dade ana tsamanin zuwan faduwar farashin kuma ana tunanin nan da kankanin lokaci zai yi daraja ya kai $60,000.

Farashin kudin intanet ya tashi a wannan shekarar, Bitcoin kadai ya karu da 400% cikin watanni 12 da suka gabata.

A farkon wannan shekarar, kwararru sun yi gargadin cewa mutane kalilan ne a duniya ke rike da mafi yawancin kudin na intanet.

Source: Legit

Online view pixel