Da Dumi: An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai

Da Dumi: An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai

  • An rufe kwallejin ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE, da ke Yola a jihar Adamawa saboda zanga-zangar dalibai
  • Daliban sun yi zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadin su game da rashin ruwa da lantarki na kwanaki a makarantar
  • Mahukunta makarantar sun ce sun umurci a fara gyaran ruwan amma duk da haka daliban ba su dena zanga-zangar ba hakan yasa suka rufe makarantar

Yola, Adamawa - Zanga-zangar dalibai da ya janyo rikici ya tilasta rufe kwallejin ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE, da ke Yola a jihar Adamawa.

Wani rahoto daga SaharaReporters ta ce daliban suna zanga-zanga ne saboda mawuyacin halin da suke ciki a makarantar da ya hada da rashin ruwa.

Da Dumi: An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai
An rufe kwallejin Ilimi ta tarayya da ke Yola saboda zanga-zangar ɗalibai. Hoto: SaharaReporters
Source: Facebook

Daga bisani zanga-zangar da aka fara ta lumana ta janyo rikici.

Read also

Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SaharaReporters ta rahoto cewa zanga-zangar ta kaceme ne a yayin da sojoji da sauran jami'an tsaro suka fara fatattakar daliban.

Zuwan jami'an tsaron ya fusata daliban suka fara cinnawa gine-gine wuta tare da fasa shaguna.

Wani dalibi, wanda ya ce a sakaya sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shafe kwanaki a kwalejin babu ruwa.

Ya kara da cewa:

"An bar mu muna rayuwa a mawuyacin hali. Ka duba, dalibai fiye da 5000 a makarantar nan muka shafe kwanaki babu ruwa. Sai mun fita cikin gari neman ruwa. Sannan muna da matsala da wutar lankarki."

Martanin mahukunta makarantar

A bangarensu, mahukunta makarantar sun amsa cewa ruwan makarantar ya samu matsala amma sun musanta cewa an bar daliban tsawon kwanaki babu ruwa.

Rajistarar kwallejin, Ahmad Gidado ya ce bututun ruwan da ke kawo ruwa makarantar ne ya lalace.

Read also

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

A cewarsa, mahukunta makarantar sun dukufa sun fara aiki nan take bayan samun rahoton matsalar ruwan a jiya (Litinin), an umurci sashin ayyuka na makarantar ta gyara ruwan, amma aka farko ranar Talata aka ga dalibai na zanga-zanga.

Gidado ya ce kwallejin na da wasu rijiyoyin burtsatse amma saboda dalibai fiye da 5000, suna amfani da tankin ruwa domin kawo ruwa makarantar saboda lalacewar bututun ruwan.

"A safiyar yau tankin ruwa tana raba wa dalibai ruwa a wuraren diban ruwa amma ba su dena zanga-zangar ba. Domin kada abubuwa su tabarbare, an yi taron gaggawa sannan aka yanke shawarar rufe makarantar.
"Hukumar makarantar ta bukaci dukkan dalibai su bar makarantar nan take a yayin da hukumomin tsaro suka iso don tabbatar da komai ya tafi dai-dai," - in ji Gidado.

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

A wani rahoton, Anthony Ojukwu, babban sakatare hukumar kare hakkin bil-adama na kasa, NHRC, ya zama babban lauyan Nigeria mai mukamin SAN.

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ojukwu na daya daga cikin lauyoyi 72 da kwamitin alfarma ta lauyoyi, LPPC, ta karrama da mukami SAN a taronta na 149 a ranar Alhamis.

Lauyoyi 130 ne aka tattara sunayensu don tantance wadanda za a yi wa karin girman na SAN tun a watan Satumba.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel