Yan bindiga sun kutsa wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Yan bindiga sun kutsa wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa kai cikin wata Coci ana tsaka da ibada a Oba Oko, ƙaramar hukumar Ewekoro
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da masu bauta mutum uku kuma sun nemi miliyoyin kuɗin fansa
  • Rundunar yan sandan jihar tace jami'anta sun bazama neman maharan tare da ceto mutanen da aka sace

Ogun - Miyagun yan bindiga sun farmaki wata coci a Oba Oko dake karamar hukumar Ewekoro, jihar Ogun, inda suka yi awon gaba da masu bauta 3.

Wakilin dailytrust ya rahoto cewa maharan sun mamaye cocin ne yayin da ake tsaka da ayyukan bauta da safiyar Lahadi.

Hakanan kuma sun yi awon gaba da mutum uku da suka haɗa da, Ifeoluwa Alani-Bello, Adebare Oduntan da kuma Mary Oliyide.

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

Yan bindiga
Yan bindiga sun kutsa kai wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3 Hoto: thecable.ng
Source: UGC

Shin sun nemi kuɗin fansa?

Wata majiya dake kusa da iyalan waɗanda aka sace, ta tabbatar da cewa yan bindigan sun tuntubi iyalansu ta wayar salula.

Mutumin yace maharan sun fara tattaunawa kan biyan kuɗin fansa, inda suka bukaci a basu miliyan N6m kafin su sake su.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar wa manema labarai da kai harin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa tuni tawagar yaƙi da masu garkuwa suka bazama neman maharan tare da ceto mutanen da aka sace.

Kakakin yan sanda ya jaddada gargaɗin hukumar yan sanda cewa mutane su daina gudanar da bauta ta musamman a wasu yankuna kebantattu saboda hakan na baiwa mahara sauki wajen sace mutane.

Read also

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

A wani labarin kuma Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas ta bada tallafin miliyan N20m ga iyalan waɗanda aka kashe a harin kasuwar Goronyo.

Gwamna Zulum na jihar Borno kuma shugaban ƙungiyar, shine ya kai ziyarar jaje da kuma miƙa tallafin a madadin takwarorinsa.

Source: Legit.ng

Online view pixel