Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah

  • Shugaba Buhari zai halarci taron zuba jari a kasar Saudiyya
  • Kusan dukkan manyan yan kasuwan Najeriya zasu halarci taron
  • Hakazalika ministoci da shugabannin hukumomi kimanin 10 zasu raka shi

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tafi kasar Saudiyya ranar Litnin, 25 ga watan Oktoba, 2021 domin halartan taron hannun jari sannan kuma yayi Ibadar Umrah.

Mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, shugaban kasan zai gana da manyan yan kasuwan Najeriya, manajojin bankuna, masana ilmin makamashi da sauransu.

Ya kara da cewa za'a kwashe kwana uku ana wannan taro.

A cewarsa:

"Shugaban kasan zai hadu da manyan yan kasuwan Najeriya... Daga cikinsu akwai Alhaji Muhammad Indimi, Alhaji Aliko Dangote, Tope Shonubi , Wale Tinubu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da Leo Stan Ekeh."

Kara karanta wannan

2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya gobe Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah
Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya gobe Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Buhari zai yi ibadar Umrah

Hadimin Buhari ya kara da cewa shugaban kasan zai gudanar Ibadar Umrah a Makkah da Madina.

Bayan haka kuma ya dawo Najeriya ranar Juma'a.

Ya kara da cewa shugaban kasan zai samu rakiyan Ministan Sadarwa, Dr. Isa Ibrahim Pantami; karamin Ministan harkokin waje, Amb Zubairu Dada; karamin Ministan man fetur, Chief Timipre Sylva.

Sauran sune NSA, Maj. Gen Babagana Monguno; Diraktan hukumar NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar; shugaban hukumar NSIA, Uche Orji da shugabar hukumar jindadin Najeriya mazauna kasashen waje, Hon. Abike Dabiri-Erewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel