Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take

Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take

  • Gwamnatin jihar Kano ta bawa makahon malami Dahuru Idris Abdulhamid aiki bayan hira da aka yi da shi a Daily Trust
  • Dahuru ya magantu gan gwagwarmayar da ya sha yayin karatu a matsayinsa na makaho da irin tallafin da mutane suka masa
  • A halin yanzu wani mai taimakon al'umma ya siya wa Dahuru gida, sannan ya samu gurbin yin karatun digiri kyauta da kuma tallafin kudin mota

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bawa Dahuru Idris Abdulhamid, makahon malami da ke koyarwa kyauta a jihar aikin yi.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Daily Trust ya wallafa wani rahoto game da Dahuru, hakan yasa mutane da dama suka san shi.

Duk da makaho ne, Dahuru, wanda ya yi karatu, ya kasance yana bada gudunmawarsa ga al'umma ta hanyar koyarwa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa kan tafiya da Shekaru a siyasa

Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take
Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Bayan Daily Trust ta wallafa labari game da shi a ranar 25 ga watan Satumban 2021, wani mai tallafawa al'umma ya siya masa gida mai daki hudu.

A wani hira da aka yi da shi a karshen mako, Dahuru ya mika godiyarsa amma ya yi kira ga gwamnati ta taimaka ta bashi aiki na dindindin.

Gwamnatin jihar Kano, ta bakin kwamishinan ta na ilimi, Muhammmad Sanusi Sai'id Kiru, ta tuntubi Dahuru a ranar Asabar bayan fitar rahoton a kansa.

An gayyaci Dahuru gidan gwamnatin Kano, inda ya gana da Ganduje.

An rahoto cewa gwamnan ya tambayi matashin makohon malamin abin da ya ke so gwamnati jihar ta yi masa, sai ya nanata rokonsa ba baya na neman a bashi aikin gwamnati na dindindin.

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Ganduje, daga bisani, ya bada umurnin a bawa Dahuru aikin koyarwa na dindindin a makarantar mutane masu bukata na musamman da ke Tundun Maliki a mataki na 7(2).

Wannan ce makarantar da Dahuru ya yi karatunsa na frimari da sakandare.

A halin yanzu Dahuru yana karatu a jami'ar National Open University of Nigeria (NOUN) inda Farfesa Uba Abdallah, tsohon shugaban jami'ar ya biya masa.

Kazalika, bayan fitar da bidiyon hira da aka yi da shi, gidauniyar Near ta dauki dawainiyar biyansa N10,000 duk wata a matsayin kudin mota har ya kammala karatunsa a NOUN.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel