Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya

Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya

  • Yan sanda sun damke matar da ta aikata laifin sayar da haifaffiyar cikinta
  • Matar ta bayyana cewa talauci ya ingizata aikata wannan laifi
  • Ta yi nadaman abinda tayi

Kudu maso gaba - Jami'an hukuma sun damke wata mata mai suna Miss Mercy Okon da ta sayar da diyarta mai wata uku da haihuwa a farashi N150,000 saboda rashin kudi.

Mercy, wacce uwa ce mai 'yaya uku ta bayyana cewa talauci ne ya ingizata sayar da jaririyarta saboda tana bukatan biyan kudi hayan gidan da take zama.

Mercy ta bayyana hakan ne yayin hirarta da Jaridar Vanguard.

A cewarta, mahaifin jaririyar ya rabu da ita lokacin cikin na wata shida kuma ba tada mai taimaka mata.

Tace:

"Ban taba yin haka ba, na sayar da diyata N150,000 don samun kudin biyan kudin haya da kuma biyan wasu bukata."

Read also

Yanzu-yanzu: Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mahaifin diyar ya yi watsi da mu cikin na wata shida, bani da wani abi kuma abubuwa sun yi tsanani, shi yasa na bayar da diyata, amma wanda ya hada ni da masu sayan jariran yace min dan'uwansa na son aurena."
"Daga nan aka bani N150,000 kuma na karba...daga baya yan sanda suka shiga lamarin kuma aka kamani."

Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya
Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya Hoto: Vanguard
Source: Facebook

Bayan ƙwace motarsa da IPhone, Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6

A wani labarin daban, Alkalin babbar kotu da ke zama a Ibadan ya yanke wa Adewale Tosin, dan damfarar yanar gizo hukuncin share harabar kotun na tsawon watanni 6.

Alkali Bayo Taiwo ya yanke wa Tosin wannan hukuncin ne bayan ya amsa laifin sa na damfarar wani bature dan Amurka.

Read also

Yadda shugaba a NIS ya yi shigan burtu ya kame jami'ansa dumu-dumu da rashawa

Har ila yau, Daily Nigerian ma ta ruwaito yadda saurayin ya dinga yaudarar baturen, Zielone Nyson a matsayin mace mai suna Lylian Zamarippa.

Sai da Taiwo ya warwari Nyson kudi dala 2,400. Don haka alkalin ya umarce shi da asubancin share kotun, inda ya ce karfe 8am ta dinga yi ma sa a harabar kotun.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel