Sarki ya kira taron gaggawa, yana barazanar tsige Hakiman da ke hada-kai da ‘Yan bindiga

Sarki ya kira taron gaggawa, yana barazanar tsige Hakiman da ke hada-kai da ‘Yan bindiga

  • Sarkin Ningi ya yi zama na gaggawa da Hakimai da Masu unguwannin kasar sa
  • Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ya yi gargadi a kan alaka da ‘Yan bindiga
  • Mai martaba yace za a binciki Masu kasar Ningi kan zargin hada-kai da Miyagu

Bauchi - Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ya gargadi duk masu sarautar gargajiya a kan hada-kai da miyagun ‘yan bindiga.

Jaridar Daily Trust tace Sarki Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ya ja-kunnen masu kasar Ninge ne a lokacin da ya yi wani zama na gaggawa da su.

Yunusa Muhammad Danyaya ya fada wa masu unguwanni da lawalai cewa zai sauke duk wanda aka samu yana bada gudumuwa wajen rashin tsaro.

“Sarakunan mu ba su da tarihin samun wata alaka da marasa gaskiya a kasar Ningi.” - Danyaya

Read also

‘Dan Majalisar APC ya rabawa mutane 2000 a mazabarsa kudi da kayan sana'a a Kano

“Na damu da na ji labari akwai masu kasan da ke hada-kai da ‘yan bindiga a wasu kananan hukumomi na jihar Bauchi, daga ciki har da Ningi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a binciki masu rike da kasa a Ningi

“Tuni mun kaddamar da kwamitin bincike domin bankado duk wanda aka samu da laifin hada kai da ‘yan bindiga, za a kori wanda aka samu da laifi.”

“Ba za mu yarda da wannan ba, ba za mu yi aiki da duk wani wanda yake da dangataka da marasa gaskiya ba domin wannan cin amanar al’umma ne.”

Rahoton yace da yake jawabi ga masu rike kasa, Mai martaba yace duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu da rashin gaskiya bai dace da rike kasa ba.

Bayan haka, Sarkin ya tabbatar da cewa za su mara wa gwamnatin jihar Bauchi baya, yace ba za su yarda wani Basarake ya yi rashin kunya ga gwamnati ba.

Read also

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Alhaji Danyaya ya bayyana cewa suna tare da gwamnatin Bala Mohammed domin gwamnan ya na bakin kokarinsa wajen wanzar da zaman lafiya a Ningi.

An samu 'yan kungiyar asiri

Kuna da labari Alkalin babban kotun taraya da ke garin Abuja ya saurari shari’ar da ake yi da wasu daliban jami'ar UNIMAID, kuma ya same su da laifi.

Kotu ta yanke masu daurin shekaru shida a kurkuku. Daga ranar 20 ga watan Oktoba ne ‘Daliban jami’ar za su fara yin zaman kaso na shiga kungiyar asiri.

Source: Legit.ng

Online view pixel