An daure dalibai 19 da aka kama sun shiga kungiyar asiri a Jami’a bayan doguwar shari'a

An daure dalibai 19 da aka kama sun shiga kungiyar asiri a Jami’a bayan doguwar shari'a

  • Kotu a jihar Borno ta samu wasu daliban UNIMAID da laifin shiga kungiyar asiri
  • Alkalin babban kotun, Umar Fadawu ya yanke masu daurin shekaru shida a tsare
  • Lauyan da ya tsaya wa ‘yan makarantar ya nemi kotu ta sassauta ukuba a kan su

Borno - A ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba, 2021, babban kotu da ke garin Maiduguri, Borno ya daure daliban da aka samu da laifin shiga kungiyar asiri.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta ce Alkali mai shari’a Umar Fadawu ya saurari wannan kara, kuma ya zartar da hukunci a zaman da aka yi a jiya.

Umar Fadawu yace an samu hujjoji masu karfi da ke tabbatar da cewa duk wadannan dalibai sun aikata laifin da ake zarginsu da sun shiga kungiyar asiri.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

Shiga ko samun mutum da hannu a ciki ko jagorantar kungiyar leken asiri ya saba wa dokar kasa.

Rahoton yake cewa jami’an ‘yan sanda sun damke wadannan dalibai da aka samu da laifi tun a ranar 21 ga watan Satumba, 2019 a wani otel a Maiduguri.

UNIMAID
University of Maiduguri Hoto: loginportals.com
Asali: UGC

Neo Black Movement ta kai su kurkuku

Mai shari’a Umar Fadawu yace sunan kungiyar ta su Neo Black Movement ko a ce mata Black Axe.

Bayan ya ji jawabin lauyan da ke kare wadanda ake kara, Ahmed Hamman, ya zartar masu da hukuncin daurin shekaru shida, ba tare da damar biyan tara ba.

Barista Hamman ya roki kotu ta yi wa wadanda yake kare wa rangwame, ya na mai nema masu afuwa. Hakan ya tabbatar da rashin gaskiyar ‘yan makarantar.

Kara karanta wannan

Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu

Sunayen wadanda aka samu da laifi

“Kotu ta yanke wa Arnold Augustine, Onu Chiduben, David Emmanuel, Awuto Abayomi, Mustapha Abulkadir, Levi Epraim, Onuebu Godspower Chibuzor, Ben Oni, Yakubu Chiroma, Mohammed Adamu, Calvin Ijafiya, Henry Michael Ujah, Chris Kallu, Totsi Samuel, Onwuka Ugochukwu, Audi Yohana, Samuel Talba, Donald Omguze da Joseph Olaiya, daurin shekaru shida na kowane laifi da ku ka aikata.
Zaman ku a gidan kaso zai fara ne daga yau, 20 ga watan Oktoba.” – Fadawu.

‘Yan matan Chibok sun shiga AUN

Dazu ku ka ji cewa tsofaffin ‘Yan matan makarantar Chibok sun shiga jami'ar American University of Nigeria da ke garin Yola, za su fara karatun digiri.

A shekarar 2014 ‘Yan ta’addan Boko Haram suka dauke daliban a jihar Borno. Bayan tsawon lokaci an ceto wasu daga cikinsu, wasu sun samu damar zuwa jami'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel