Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya

Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya

  • Hotuna da bidiyon macijin da ya fi kowanne girma a duniya ya gigita masu kallo tare da bada mamaki
  • An tsinta dankareren maciji a gandun dajin Dominica da ke US yayin da ake gyara wurin
  • Kamar yadda aka ga bidiyon da hotunan, macijin zai kai tsayin kafa goma bayan an daga shi da mota

Hotuna da bidiyo sun bayyana gagarumin dankararen macijin da ya fi kowanne girma a fadin duniya ana daga shi da mota.

Dankareren dabban an tsince shi ne yayin da wasu ma'aikata suke gyara tare da kakkabe gandun dajin Dominica, jaridar the-sun news ta US ta wallafa.

Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya
Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya. Hoto daga the-sun.com
Asali: UGC

A bidiyon da ya bayyana, mutumin da ke nadar bidiyon cike da mamaki tare da al'ajabi aka ji ya na cewa: "Wayyo mahaifiyata, mene ne wannan?"

Kara karanta wannan

Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

Katon macijin wanda a kalla ya fi taku goma a tsayinsa, an gan shi da ran shi kuma an daga shi ne da motar haka manyan ramuka.

Tun bayan da aka wallafa bidiyon a kafafen sada zumuntar zamani a makon da ya gabata, bidiyon ya ja hankula inda miliyoyin mutane suka dinga kallo cike da mamaki.

Da yawa daga cikin masu kallo sun nuna mamakinsu kan girman dabban.

Wani ya ce:

"Wannan ya yi kama da wani irin tarihin duniya.

Wani kuwa wallafa yayi ya na cewa:

"Tabbas, wannan abun kato ne."
Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya
Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya. Hoto daga the-sun.com
Asali: UGC

Har yanzu ba a gane wanne irin maciji ne ya bayyana a bidiyon.

Gandun dajin Dominica wuri ne mai fadin mil 29 a tsayi da kuma mil 16 a fadi. Ana kallonsa a tsibirin da ke dauke da yanayi mai kyau domin irin namun daji da ake gani.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Daya daga cikin irin macijin da ake samu a tsibirin shi ne maciji mai matukar hatsari da ake kira da "boa constrictor" wanda ke girma har ya kai kafa 13.

A yayin kai farmaki, macijin na cizo da hakoransa kafin daga bisani ya nade mutum ko dabba da jikinsa tare da matse shi har ya mutu, The Sun US ta wallafa.

Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya
Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya. Hoto daga the-sun.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel