Shugaban jami’ar tarayya guda yana karbar N100,000 a matsayin albashin wata a IPPIS

Shugaban jami’ar tarayya guda yana karbar N100,000 a matsayin albashin wata a IPPIS

  • Farfesa Sulyman Age Abdulkareem yace ana samun matsala da tsarin IPPIS
  • Albashin karamin malami ake biyan shugaban jami’ar UNILAG a duk wata
  • Malaman jami’a suna ta kuka tun da aka koma biyan su da manhajar IPPIS

Kwara - Shugaban jami’ar tarayya ta Ilorin, Farfesa Sulyman Age Abdulkareem, yace ana biyansa albashin karamin malami bayan fara amfani da IPPIS.

A maimakon a biya shi cikakken kudinsu a karshen wata, Farfesa Sulyman Age Abdulkareem yace yana tashi da albashin da ake biyan kananan malamai.

Nigerian Lawyer ce ta rahoto Sulyman Age Abdulkareem yana cewa ya rasa kashi 500% na kudin da ya kamata ya rika karba a matsayin shugaban jami’a.

Jami’ar Ilorin ta na cikin manyan makarantun tarayya, kuma ta na cikin wadanda ta fi yawan dalibai.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

Shugaban jami’ar ya yabi manhajar ta IPPIS a dalilin dabarun da aka shigo da shi, amma yace manhajar ta kawo masu matsaloli a maimakon ayi gyara.

Jmi’ar tarayya
Jami'ar UNILORIN Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Abin da aka kawo domin ya magance matsaloli bai kamata ya rika kirkiro wasu matsalolin ba.”
“Za ku yi mamaki ku ji cewa albashin mafi kankanta malami ake biya na a maimakon na shugaban jami’a kamar yadda ya kamata a IPPIS.” – Age Sulyman.

Legit.ng Hausa ta yi bincike ta gano cewa abin da ake biyan karamin malami bai wuce N120, 000 ba. Amma abin da ke shiga hannunsu bai zarce N106, 000.

Farfesan yana sa rai za a shawo kan matsalar da ake fuskanta ba da dade wa ba, yace kalubalen da ake fuskanta ya fi shafar ma’aikatan da ke koyar wa a aji.

Kara karanta wannan

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

Farfesa Abdulkareem ya kuma bayyana cewa bai yi nadamar yin sulhu da kungiyar malaman jami’an na ASUU ba, yace yin hakan ya ceci makarantar.

George Weah ya karrama Emmanuel Tolue

A yau aka ji wani matashi mai shekara 18 da yake zaman banza ya tsinci sama da Naira miliyan 20, ya ba mai su. Wannan abu ya faru ne a kasar Liberiya.

Matashin da ya maida kudin ya samu kyautar N4.1m a hannun shugaban Liberiya. Bayan kudin da ya samu, ya samu damar yin karatu har zuwa Digirgir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel