‘Dan shekara 18 ya dawo da N20.5m da ya tsinta, ya samu kyautar miliyoyi da abubuwan alheri

‘Dan shekara 18 ya dawo da N20.5m da ya tsinta, ya samu kyautar miliyoyi da abubuwan alheri

  • Wani matashi mai shekara 18 ya tsinci sama da Naira miliyan 20, ya ba mai su
  • Emmanuel Tuloe ya maida wa wata mata $50, 000 dinta da ya tsinta a Liberiya
  • Wannan ya sa Tuloe ya samu kyautar kudi da damar karo karatu a makaranta

Liberia - George Weah ya yi alkawarin karrama wani matashi mai gaskiya, Emmanuel Tuloe, wanda ya tsinci Dala 50000, kuma ya maida kudin ga mai su.

Liberian Observer tace shugaban kasa George Weah zai ba Emmanuel Tuloe babbar lambar yabo na kasa saboda irin wannan gaskiya da amanar da ya nuna.

Haka zalika shugaban na kasar Liberiya zai dauki nauyin karatun matashin har matakin digirgir. Emmanuel Tuloe ne zai zabi makarantar da yake so ya halarta.

Read also

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Emmanuel Tuloe zai samu N410m, babura 2, lambar yabo da ilmi

“Ni a karon kai na da iyali na, na ba shi wannan damar karatu, ko ina kan mulki, ko ba na nan.” – Weah.
“Ina so in sanar da kai cewa a bikin kasa na gaba da za ayi, za a karrama ka da daya daga cikin mafi girman lambar yabo saboda tsabar gaskiyarka.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bugu da kari, ina mai damka maka kyautar Dala 10, 000 da kuma sababbin babura domin su tallafa wa halin tattalin arzikin da ka ke ciki.” – Weah.
‘Dan shekara 18 ya dawo da N20.5m da ya tsinta, ya samu kyautar miliyoyi da abubuwan alheri
Emmanuel Tuloe Hoto: BBC.co.uk, The Executive Mansion
Source: UGC

Yadda Tuloe ya tsinci Dalolo a titi

Tuloe mai shekara 18 wanda ba ya zuwa makaranta ya taki wannan sa’a a dalilin wata mata da ya maida wa kudinta da ta bari kan titi a yankin Nimba County.

Read also

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Matashin yace yana tuka babur a hanya sai ya ga tulin kudi a cikin leda, sai ya dauka domin ya yi cigiya. A ranar sai ya ji wata Baiwar Allah tana cigiya a rediyo.

“Wannan mata, Musu Yancy ta fito tana kuka, tana rokon duk wanda ya tsinci kudin ya dawo mata da su, saboda haka na kai mata abin ta.” - Tuloe.

Falalu Dorayi ya fito da shirin Musabbabi

A makon jiya aka fito da wani fim da aka yi kan Boko Haram mai suna Musababbi. Audu Bulama Bukarti ya yabi sabon wasan kwaikwayon, yace fim din ya yi kyau.

An nuna yadda kudi ya yi amfani sosai wajen jawo hankalin matasa cikin harkar ta’addanci.

Source: Legit

Online view pixel