Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki

  • Jami'an tsaro sun watsawa matasa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa
  • Wannan biyo gabayn gargadin da kwamishanan yan sanda yayi
  • An damke mutane da dama cikin wadanda suke gudanar da zanga-angar

Lekki - Jami'an yan sanda a ranar Laraba sun tarwatsa matasan dake zanga-zangar tunawa da EndSARS dake gudana a Lekki Toll Gate, jihar Legas.

Jami'an yan sandan sun watsawa matasan barkonon hayaki wanda aka fi sani da Tiya Gas don tarwatsa taron, rahoton ChannelsTV.

A yanzu matasan sun gudu daga wajen.

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Hotunan yadda 'yan sanda suka yi ram da masu zanga-zanga a Lekki Tollgate

Yan sanda sun yi ram da mutanen da ke zanga-zanga a Lekki tollgate a Legas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun damke wani ɗauke da makami a cikin masu zanga-zanga

Duk da jan kunnen da aka yi wa masu son yi tattakin cika shekara daya da yin asalin zanga-zangar, sun fito kwan su da kwarkwatarsu.

A safiyar Laraba, wasu mutane sun taru a tollgate inda jami'an tsaro a shekarar da ta gabata suka tarwatsa taron.

Hakeem Odumosu, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas tun farko ya ce jami'ansa su bar ababen hawa ne kadai a yankin Lekki ba wata zanga-zanga ba.

Tuni ya tura jami'an tsaro inda suka mamaye wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel